Yan Sanda Sun Kama Malaman Musulunci 3 da Zargin Fille Kan Wani a Jihar Oyo

Yan Sanda Sun Kama Malaman Musulunci 3 da Zargin Fille Kan Wani a Jihar Oyo

  • Dubun wasu malaman addinin Musulunci ta cika bayan kama su da jami’an ‘yan sanda su ka yi da zargin fille kan wani mutum a jihar Osun
  • Wadanda ake zargin su uku sun yaudari marigayin ne da nufin ba shi aiki inda su ka yi amfani da wannan damar wurin aikata abin da su ka shirya
  • Malaman wadanda aka bayyana da manya a tsakanin malaman yankin sun aikata haka ne a Moniya da ke karamar hukumar Akinyere da ke jihar

Jihar Oyo– Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta kama wasu malaman Musulunci uku kan zargin fillewa wani kai.

An tsare wadanda ake zargin ne a bangaren binciken manyan laifuka na CID da ke Ibadan babban birnin jihar.

Yan sanda sun cafke malaman Musulunci uku kan zargin fille kan wani
Yan Sanda sun kama malaman Musulunci uku a Oyo. Hoto: The Guardian.
Asali: Twitter

Meye ake zargin malaman a kai?

Punch ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun yaudari mutumin mai matsakaicin shekaru a Moniya da ke karamar hukumar Akinyere da ke jihar.

Kara karanta wannan

Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin an tabbatar da cewa ya na aiki ne ga daya daga cikin malaman inda su ka yi amfani da cewa za su ba shi aiki inda su ka aikata masa haka.

An kama malaman ne a Apepe da ke karamar hukumar Ido a cikin jihar inda mutane su ka nuna kaduwarsu kan lamarin, Phenomenal ta tattaro.

Meye mutane ke cewa kan malaman?

Wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce :

“Abin takaici ne ganin yadda daya daga cikin ma su kisan shahararren malami ne wanda ke da daraja a tsakanin malamai.”

Wata majiya ta tabbatar da cewa wadanda ake zargin su na da gidajen haya a yankin inda kuma su ka aikata laifin a Moniya.

Majiyar ta ce:

“An dauke sharia’r zuwa bangaren binciken manyan laifuka da ke Iyaganku don kara samun bayanai.”

Kara karanta wannan

Matashi Ya Shiga Hannu Kan Zargin Yunkurin Kisan Almajiri Bayan Malaminsu Ya Lalata Neman Aurensa

Mutanen yankin sun nuna damuwa kan yadda wadannan ma su shigar addinin su ka aikata irin wannan danyen aiki.

Yan sanda sun kama mata da hallaka ‘yar kishiyarta

A wani labarin, jami’an ‘yan sanda sun cafke wata mata da zargin hallaka ‘yar kishiyarta a jihar Bauchi.

Wacce ake zargin mai suna Khadija Adamu ta roki afuwar hukumomi inda ta ce iyayen yarinyar sun yafe mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.