Gwamnatin Legas Ta Rufe Masallaci, Coci-Coci da Wuraren Tarurruka Kan Damun Jama’a
- Gwamnatin jihar Legas ta sanar da rufe wasu coci-coci da masallaci a wasu yankuna da ke jihar saboda shiga hakkin mutane
- Hukumar Kula da Muhalli ta jihar, LASEPA ita ta gudanar da wannan gagarumin aiki saboda yawan korafi da ake yi na damun jama’a
- Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa, Tokunbo Wahab shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter
Jihar Legas – Gwamnatin jihar Legas ta rufe wasu coci-coci da masallaci da kuma wuraren tarurruka a jihar saboda damun mutane da kara.
Hukumar Kula da Muhalli ta jihar (LASEPA) ita ta rufe wuraren ibadar da kuma wuraren tarurruka saboda shiga hakkin jama’a da su ke yi da kararraki.
Wane mataki Legas ta dauka kan masallaci da coci?
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa a jihar, Tokunbo Wahab shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter a yau Asabar 21 ga watan Oktoba, cewar Tribune.
Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wahab ya ce babban manajan hukumar, Tunde Ajayi shi ya jagoranci wannan aiki kan wuraren ibada da tarurruka saboda shiga hakkin jama’a da kuma kawo cikas ga muhalli.
Daga cikin wuraren da abin ya shafa akwai masallacin Ansar-Ud-deen da Cocin Restoration Global Centre, cewar Vanguard.
Sauran sun hada da wurin taro na Bloomberg da Club Hexagon da wurin shakatawa na Starrex da ke Agbada sai kuma Bayrock a Lekki Phase 1.
Wane martani mutane ke yi kan rufe masallacin da coci?
Wannan na zuwa ne yayin da mutane ke korafin cewa ana shiga hakkinsu da sautuka yayin da su ke cikin hutawarsu a cikin gidajensu.
Hukumar ta dauki wannan mataki ne don tabbatar da bai wa wadanda ake zalunta hakkinsu na ‘yan kasa
Sai dai mutane da dama sun yi korafi inda su ke cewa babu wani masallaci da aka kulle kawai iya coci-coci da wuraren tarurruka aka rufe.
FCDA ta musanta rushe bangaren Masallacin Abuja
A wani labarin, ana zargin Hukumar Gudanarwa a Abuja, FCDA na shirin rushe wani bangare na babban masallacin Abuja.
Sai dai hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta musanta hakan inda ta ce babu kamshin gaskiya a ciki.
Daga bisani kwamitin masallacin shi ma ya fitar da sanarwa inda musanta rade-radin.
Asali: Legit.ng