Babban Birnin Tarayya: Wike Ya Amince a Kwace Gidajen Da Aka Sauya Manufar Ba Da Su

Babban Birnin Tarayya: Wike Ya Amince a Kwace Gidajen Da Aka Sauya Manufar Ba Da Su

  • Hukumar Babbar birnin tarayya (FCTA) za ta kwace wasu kadarori a Abuja kwanan nan
  • An tabbatar da ci gaban ne a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, bayan wata sanarwa da Mukhtar Galadima, daraktan kula da ci gaban FCTA ya fitar
  • Da amincewar ministan, za a soke gidajen da aka sauya akalar amfaninsu zuwa wani daban maimakon manufar da aka amince da shi

FCT, Abuja - Hukumar babbar birnin tarayya karkashin jagorancin Nyesom Wike ta sanar da aniyarta na kwace wasu gidaje da aka siyar a baya domin mayar da su matsugunin al'umma amma aka sauya akalar amfaninsu zuwa wani daban.

Mukhtar Galadima, daraktan kula da ci gaban babban birnin tarayya, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

Ya yi bayanin cewa a 2005, gwamnatin tarayya ta fara shirin samar da kudaden shiga na sayar da gidaje ga mazauna yankin domin tabbatar da ci gaban su.

Wike ya amince da kwace wasu gidaje a Abuja
Babban Birnin Tarayya: Wike Ya Amince a Kwace Gidajen Da Aka Sauya Manufar Ba Da Su Hoto: FCTA/Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Sai dai kuma, wadanda suka mallaki kadarorin da dama sun sauya manufar wadannan gidaje zuwa wani daban, lamarin da hukumar FCTA ba za ta ci gaba da lamunta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka saba ka'ida za su biya tarar keta ka'ida, inji jami'in FCTA.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Galadima ya ce:

"A kan haka ne ministan ya amince sannan ya yi umurnin cewa dukkan mamallakan irin wadannan kadarori su mayar da shi zuwa ainahin abun da aka tsara ayi da filin, wanda yake matsugunin al'umma.
“Ministan ya kuma umurci masu kadarorin, musamman a kan manyan tituna da suka mayar da kadarorinsu zuwa wani amfani na daban ba tare da izini ba, ko dai su mayar da shi zuwa ainahin abun da aka ce ayi da shi ko kuma su biya tara.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

"Rashin bin wannan umarnin zuwa ranar 1 ga Nuwamba, za a dauki gidan a matsayin wanda aka soke sannan a mayar da shi ga FCTA."

Ya yi nuni da cewa sashen ya kwashi bayanan gidaje fiye da 111 da aka sauya akalar amfani da su game da gidajen da aka siyar.

Kwamitin masallacin Abuja ya karyata jita-jitar cewa za a rushe bangaren masallacin

A wani labarin, kwamitin babban masallacin Abuja ya bukaci al'ummar Musulmi da su guji bata sunan ministan Abuja, Nyesom Wike.

Limamin masallacin, Dakta Muhammad Kabir Adam da daraktan kudi, Ambasada Haliu Shu'aib su suka bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng