Musulunci Ya Samu Karuwa: Matashiya Yar Shekaru 18 Ta Karbi Addinin Musulunci

Musulunci Ya Samu Karuwa: Matashiya Yar Shekaru 18 Ta Karbi Addinin Musulunci

  • Kullun burin kowani addini shine a ce yana yaduwa da samun karuwa a cikin al'umma
  • Wata matashiyar budurwa mai suna Blessing ta bar addininta na kiristanci inda ta karbi Musulunci
  • Matashiyar mai shekaru 18 ta sauya sunanta inda a yanzu ta koma Khadijah

Musulmai da Kiristoci kan kasance cikin farin ciki a duk lokacin da aka samu wani da ya karbi addininsu tare da bin tafarkin da suke kai.

Kamar yadda Kiristoci ke yada addinin Kirista, kuma a rungumeshi, haka suma musulmai suke yi ba tare da sassautawa ba.

A hakan kuwa kowanne lokaci ake samun wadanda ke sauya addinin da suke bi da farko zuwa wani daban.

Cikin haka ne addinin Musulunci ya samu karuwar wata matashiyar budurwa yar shekaru 18, wacce ta bar addininta na kiristanci sannan ta karbi musulunci.

Kara karanta wannan

"Ga Kyau, Ga Kuruciya”: Dan Najeriya Ya Tarbi Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya a Filin Jirgin Sama, Bidiyo

Blessing ta karbi musulunci
Musulunci Ya Samu Karuwa: Matashiya Yar Shekaru 18 Ta Karbi Addinin Musulunci Hoto: @MFaarees_.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyakkyawar budurwa mai suna Blessing ta sauya sunanta inda ta koma 'Khadijah' a yanzu.

Shafin @MFaarees_ ne ya sanar da wannan labari a dandalin X wacce aka fi sani da Twitter a baya.

Ya kuma wallafa hotunan matashiyar wanda ke nunata a lokacin da take kirista sanye da riga da wando da kuma wanda ta dauka bayan ta zama Khadijah sanye da hijabi.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Wata kirista mai shekaru 18 ta musulunta.
"Ta sauya sunanta daga Blessing zuwa Khadija.
"Allah ya karbi musuluncinta ya kuma sa ta tabbata a cikin addininta.
"Barka da zuwa addinin gaskiya da zaman lafiya yar uwa. ❤"

Ga wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani bayan budurwa ta musulunta

Legit Hausa ta tattaro martanin jama'a a kan musuluntar Khadijah inda yawanci suka yi mata maraba da shigowa addinin musulunci. Ga martanin a kasa:

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

@aminuArgungu ya yi martani:

"Allah ubangiji ya karfafa imaninta da Allah sannan yasa ta zamo Musulmah ta gari. Ameen."

@Iam_abdulwaasi ya ce:

"Turo da bayananta ina bukatar matar aure..."

@ilaah0 ya ce:

"Ta yi kyau a musulunci."

@_Adam_breezy Ya ce:

"Allahu Akbar. Ameen ya Allah."

@SireAbk ya ce:

"Masha Allah, Allah ya karfafa imaninta da namu."

“Ka tsayar da kiyayyar”: Reno Omokri ya wayar da kan Sheikh Gumi bayan ya kira Wike “shaidani”

A wani labarin, Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi martani ga furucin da fitaccen malamin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya yi.

Ku tuna cewa Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a matsayin shaidanin mutum.

Gumi ya yi furucin ne yayin da yake watsi da tarban ambasan Isra'ila a Najeriya da Wike ya yi a ofishinsa da kuma shirin hada kai da Isra'ila kan lamarin tsaro a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng