“Kyakkyawa”: Bidiyon Wata Mata Mai Tarin Gemu Kamar Na Maza Ya Dauka Hankali

“Kyakkyawa”: Bidiyon Wata Mata Mai Tarin Gemu Kamar Na Maza Ya Dauka Hankali

  • Wata farar mata mai halittar fuska ta musamman ta saki wani bidiyo tana mai nunawa duniya gemun da ke fuskarta
  • Matashiyar Sarah Anane, ta ba yan TikTok mamaki, inda da dama daga cikinsu suka ce tana kama da namiji saboda gemun da ke fuskarta
  • Sarah ta shahara a TikTok, inda take da mabiya fiye da 24k, da dama daga cikinsu suna sha'awar gashin fuskarta

Wata matashiya ta yi fice a TikTok bayan ta saki wani dan gajeren bidiyo don nunawa mutane gemun da take dauke da shi a fuskarta.

Kyakkyawar matar, Sarah Anane, ta ja hankalin muane saboda fuskarta na dauke da gemu kamar na maza.

Mata mai dauke da gemu a fuska
“Kyakkyawa”: Bidiyon Wata Mata Mai Tarin Gemu Kamar Na Maza Ya Dauka Hankali Hoto: TikTok/@sarahanane758.
Asali: TikTok

Sarah ta daura bidiyoyi da dama a shafinta tana mai nunawa duniya fuskarta ta musamman, wanda ke cike da gashi.

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Matar da Bata San Ta Na Da Juna Biyu Ba Ta Haifi Jaririya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Gashin fuskar Sarah ya sa ta yi fice a dandalin, inda a yanzu haka take da mabiya 24k.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daya daga cikin bidiyoyinta, an gano Sarah tana rera waka mai dadi wanda ke tashi daga kasa.

Mabiyanta da dama da suka yi martani kan bidiyon sun bayyana ta a matsayin kyakkyawar mata, cewa gashin ya sa ta kara kyau.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@SWEETLINDA ta ce:

"Allah ya yi albarka, masoyiya."

@Edwige Queen ya ce:

"Yana karfafamu, yar'uwata."

@Cherub Beaver The Prefect ya ce:

"Ya yi matukar kyau. Ina son mace mai gashi."

@prayersisthekey ta ce:

"Kina da kyau, masoyiyata."

@commerrme ta yi martani:

"Wayyo Allah na, me ya faru a nan."

@Westhold_Williamya tambaya:

"Don Allah zan iya kasancewa tare da ke?"

@Abhena Slime ta yi martani:

"Amma dai akalla kina iya askewa."

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

@joeboydethinker1 ya ce:

"Ina matukar sonki, sarauniya."

Yadda gemu ya fitowa wata kyakkyawar budurwa, mijinta ya rabu da ita

A wani labarin, mun ji cewa mijin Mandeep Kaur ya rabu da ita yan shekaru bayan aurensu sakamakon gemu da ya fara fito mata a fuska.

Kaur ta shiga wani yanayi bayaj mijinta wanda take kallo a matsayin sahibin ranta ya rabu da ita saboda gemun da ya fitar mata a fuska.

A cewar Mayo Clinic, ‘hirsutism’ wani yanayi ne a jikin mata wanda ke sa gashi mai yawa ya fitar masu a fuska, kirji da baya kamar maza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng