Gwamna Abba Gida Gida Na Kano Ya Dauki Nauyin Dalibai 1001 Zuwa Kasashen Duniya Karo Karatu

Gwamna Abba Gida Gida Na Kano Ya Dauki Nauyin Dalibai 1001 Zuwa Kasashen Duniya Karo Karatu

  • Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin dalibai 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatu
  • Gwamna Abba Kabir na jihar shi ya kaddamar da wannan shiri wanda tsohon gwamna Kwankwaso ya kirkiro
  • Kwankwaso ya shawarci masu cin gajiyar da su yi iya yinsu don ganin sun amfani al’ummar jihar da kasa baki daya

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya dauki nauyin karatun dalibai 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda.

Abba Gida Gida shi ya bayyana haka yayin kaddamar shirin na tallafin karatun daliban a gidan gwamnatin jihar a jiya Alhamis 19 ga watan Oktoba.

Abba Kabir ya dauki nauyin karatun dalibai 1001 zuwa kasashen waje
Gwamna Abba Kabir Dauki Nauyin Dalibai 1001 Zuwa Kasashen Duniya. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Meye Abba Gida Gida ke cewa kan tallafin karatun?

Abba ya ce tallafin karatun dalibai zai fara ne da dalibai guda 550 a karon farko kafin a ci gaba daga baya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kwankwaso Da Abba Su Na Raba Wa Daliban Kano ‘Daloli’ a Jirgi Kafin Tafiya Indiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan shiri an faro shi ne tun lokacin mulkin Sanata Rabiu Kwankwaso inda ya ce hakan ya inganta Kano da kasa baki daya.

Ya ce:

“A bayyane ya ke yanzu wadanda su ka samu tallafin karatu a lokacin mulkin Kwankwaso su na rike da manyan guraben aiki a wannan gwamnati.”

Daga cikin wadanda tsohon gwamnan ya dauki nauyinsu akwai kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar, Dakta Yusuf Ibrahim Kofarmata.

Sauran sun hada da Daraktan kididdiga ta jihar, Farfesa Aliyu Isa Aliyu da kuma hadimin gwamna, Dakta Bashir Muzakkir da sauransu.

Gwamnan ya kara da cewa:

“Wannan shirin na daukar nayuyin dalibai zuwa kasashen waje karo karatu, mai gidanmu, Sanata Rabiu Kwankwaso ne ya kirkiro.
“Mai girma sanatan ya dauki nauyin kaso uku na dalibai zuwa kasashe akalla 16 a fadin duniya.
“Wannan shiri na daukar nauyin dalibai ya samar da kwararru da masu digirin digir-gir a bangaren kiwon lafiya da tukin jirgi da kere-kere da sauransu.”

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Tona Komai, Ya Fadi Ainihin Masu Hana a Gyara Lantarki a Najeriya

Meye martanin Kwankwaso kan tallafin karatun?

A martaninshi, Rabiu Kwankwaso ya yabawa gwamnatin jihar da wannan kokari na ci gaba da wannan tsari.

Tsohon gwamnan ya shawarci wadanda su ka ci gajiyar da su yi abin da ya dace da kuma zama masu amfanin al’umma.

Ana saran kashin farko dalibai 550 za su tashi a yau Juma’a bayan karbar dukkan takardun da su ka dace na tafiyar.

Fasto ya yi hasashen wanda zai yi nasara a Kano

A wani labarin, Fasto Elijah Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce za ta yi nasara a kotun zaben jihar Kano.

Faston ya bayyana haka ne a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba a cikin wani faifan bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.