Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 5 a Wani Hari a Jihar Benue
- Wasu tsagerun ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum biyar a wani ƙazamin harin da suka kai a jihar Benue
- Ƴan bindigan sun kai harin ta'addancin ne a ƙauyen Ayilamo da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta bayyana cewa ta ƙara jami'an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya
Jihar Benue - Miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan harin ta'addanci a jihar Benue inda suka halaka mutum biyar.
Jaridar PM News ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai farmakin ne a ƙauyen Ayilamo da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar ranar Laraba, 17 ga watan Oktoban 2023.
Menene abin da ƴan sanda suka ce kan harin?
Sewuese Anene, kakakin rundunar ƴan sanda a jihar ta yankin Arewa ta Tsakiya ta tabbatar da aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anene ta ƙara da cewa tsirarun mutane sun samu raunuka a yayin harin, rahoton Jaridar The Punch ya tabbatar.
Kakakin rundunar ƴan sandan ta ce an sake kai wani hari a unguwar Mbachohon da ke ƙaramar hukumar Gwer-West, amma ta bayyana cewa babu cikakken bayani kan harin.
Rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa an kashe mutane shida a harin na Mbachohon.
"Hare-haren abin takaici ne, Ana kara tura jami’an tsaro a yankunan domin dawo da zaman lafiya,” A cewar Anene.
Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Kebbi
Yan bindiga sun aikata aikin ta'addanci a ƙauyen Kanzanna na ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi a wani ƙazamin hari da suka kai.
Tsagerun ƴan bindigan sun halaka bayin Allah mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu mutum uku waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, a yayin harin da suka kai a ƙauyen.
Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga
A wani labarin na daban kuma, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka miyagun ƴan bindiga mutum uku a wani farmaki da suka kai musu a yankin Udowa cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Dakarun sojojin dai sun yi wa ƴan ta'addan kwanton ɓauna ne tare da buɗe musu wuta, wanda hakan ya sanya suka samu nasarar sheƙe mutum uku daga cikinsu da ƙwato makamai masu yawa.
Asali: Legit.ng