Ido Zai Raina Fata da ‘Yan Majalisa Su Ka Dauko Binciken Kudin Tallafin COVID-19

Ido Zai Raina Fata da ‘Yan Majalisa Su Ka Dauko Binciken Kudin Tallafin COVID-19

  • ‘Yan Majalisar wakilan tarayya sun yi magana a kan zargin karkatar da kudin da aka yi tanadi yayin annobar COVID-19
  • Nyampa Zakari ya zargi cewa makudan biliyoyin da aka ware sun yi kafa daga wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati
  • Majalisa ta gamsu da batun da Hon. Nyampa Zakari ya gabatar, kwamiti na musamman zai yi bincike cikin kwanaki 28

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta umarci Kwamitin Asusun Gwamnati ya yi duba a kan zargin karkatar da kudin tallafin annobar COVID-19.

P/Times ta ce a ranar Talata da aka zauna a majalisar wakilai, Nyampa Zakari (PDP Adamawa) ya bijiro da zargin an karkatar da kudin tallafin.

'Yan majalisa
'Yan majalisa za su binciki tallafin COVID-19 Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

COVID-19: Majalisa ta ce an taba N183.9bn

‘Dan majalisar yake cewa gwamnatin tarayya ta ware N183.9bn daga kasafin kudi domin bada taimako lokacin da mummunar cutar ta barke.

Kara karanta wannan

Sarki Mai Martaba Ya Tona Asiri, Ya Ce N28,000 Ake Ba Sarakuna Duk Wata, Gwamnan PDP Ya Maida Martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Nyampa Zakari ya ce hukumomin duniya ne su ka bada gudumuwar tallafin kudin.

"Jimillar N83.9bn aka ware domin yakar COVID-19 a kasafin kudin shekarar 2020, sai kuma sama da N100bn a kwarya-kwarya kasafin ta hannun hukumomin bada taimako na duniya.

- Hon. Nyampa Zakari

An rahoto ‘dan siyasar ya na cewa gwamnatin tarayya ta fito da tsare-tsare barkatai a lokacin saboda a farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Abin da ya tunzuro 'Yan majalisa

Zakari ya ce an fahimci an karkatar da kudin ne daga rahoton mai binciken kudi na kasa, hakan ya sa aka ga bukatar a zurfafa bincike.

Rahoton Odita Janar da wasu bayanai sun nuna kaso mai tsoka na kudin da aka ba Najeriya gudumuwa sun bi iska a ma’aikatu (MDA).

Sauran ‘yan majalisa irinsu Ahmed Jaha (APC Borno) sun yarda da bukatar ayi bincike domin hukumomi su san inda kudin su ka shiga.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

A karshe Abbas Tajudeen ya yarda a binciki lamarin, sai a gabatar da rahoto a mako hudu. Kwamitin zai gama aikinsa nan da Nuwamba.

Za a rabawa talakawa kudi

Ana da labari Gwamnatin tarayya ta ci bashin $800m daga bankin Duniya saboda cire tallafin fetur ya jawo karin tsadar rayuwa a kasa.

Halima Shehu ta fadawa Majalisa hukumar NSIPA za ta raba N5000 ga wadanda ba su da hali da kuma jarin N150, 000 ga ‘yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng