Yabon gwani ya zama dole: Jahohi guda 3 da suka ciri tuta wajen yaki da COVID19 a Najeriya
A yanzu dai kam ba sabon labari ne yadda annobar Coronavirus ta bulla a Najeriya, da kuma yadda take cigaba da ruruwa a tsakanin jahohin kasar tana yi ma jama’a dauki daidai.
Sai dai baya ga kokarin da gwamnatin tarayya ke yi, akwai gwamnatocin wasu jahohi da suka ke tabukawa sosai tare da bada himma wajen yaki da yaduwar Coronavirus a jahohinsu.
KU KARANTA: Mace-mace a Kano: shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 ya rasa mahaifinsa
Legit.ng ta zaro muku 3 daga cikin wadannan gwamnoni tare da irin hubbasan da suke yo domin tabbatar da sun dakile yaduwar cutar tare da kare jama’ansu.
Legas:
Gwamnan jahar Legas Babajide Sanwo Olu ya kafa kwamitin yaki da cutar Coronavirus mai karfi wanda ta kunshi zakakuran mutane da suka san abin da suke yi.
Jahar Legas ta samar da cibiyoyin gwaji guda 3; asibitin koyarwa na jami’ar Legas, Cibiyar binciken magunguna ta Najeriya da kuma Lagos State Bio-safety Lab.
Sai dai duk da haka jahar na mutane 931 da suka kamu da cutar, 192 sun warke yayin da wasu guda 21 suka mutu.
Kaduna:
Kwamitin yaki da COVID-19 na jahar Kaduna yana karkashin mataimakin gwamnan jahar ne, Hajiya Hadiza Balarabe, kwararriyar likita da ta kwashe tsawon lokaci tana aikin likitanci.
Zuwa yanzu jahar na da mutane 32 da suka kamu da cutar, an sallami 6 kuma babu wanda ya mutu a sanadiyyar cutar a jahar.
Ko a lokacin da gwamnan yake jinya bayan kamuwar sa cutar, Hajiya Hadiza baya gajiya ba wajen gudanar da jagoranci, musamman samar da wuraren killace masu cutar Coronavirus.
Daga cikin kokarin da kwamitin ta yi shi ne na samar da cibiyoyi guda uku da suke bukata NCDC ta amince dasu don yin gwajin cutar, a yanzu haka NCDC ta amince da guda 2, saura 1.
Jahar Oyo:
Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde na daga cikin gwamnonin Najeriya da suka yi fama da cutar COVID-19 sakamakon kamuwa da yayi da ita, inda ta kwantar da shi tsawon kwanaki 7.
Makinde, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar Coronavirus na jahar Oyo ya bayyana cewa a yayin da yake jinya, yana yawan shan zuma da habbatissaudah.
Gwamnan yace suna kokarin sayo sinadaran yin gwajin domin sanin matsayin sakamakon gwajin mutane 300 da suke hannu.
Daga cikin mutane 775 da aka yi ma gwajin cutar a jahar, an tabbatar da kamuwar mutane 21, yayin da mutane 2 suka mutu.
A kokarinsa na dakile cutar, gwamnan ya samar da wata cibiyar gwaji a kan hanya wanda kowa zai iya shiga kai tsaye a dauke abin da ake bukata na gwada shi, kuma ya jira sakamako.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng