Sheikh Goni Aisami: Kotu Za Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Sojojin da Suka Halaka Babban Malamin

Sheikh Goni Aisami: Kotu Za Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Sojojin da Suka Halaka Babban Malamin

  • Bayan kwashe dogon lokaci ana shari'a kan waɗanda suka halaka Sheikh Goni Aisami, kotu ta shirya sanya ranar yanke hukunci
  • Wata babbar kotun jihar Yobe da ke ƙaramar hukumar Potiskum wacce ke sauraron ƙarar ta kammala tattara dukkanin shaidu da hujjoji
  • Ana dai zargin wasu sojoji biyu ne da laifin halaka babban malamin addinin musuluncin lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Gashua

Jihar Yobe - Wata babbar kotun jihar Yobe da ke zamanta a ƙaramar hukumar Potiskum na shirin yanke hukunci a kan wasu sojoji biyu da suka kashe Marigayi Sheikh Goni Aisami bayan kammala sauraren bayanai kan shari'ar.

Shari’ar wacce ake tsakanin gwamnatin jihar Yobe da wasu sojoji biyu, Kofur John Gabriel da Adamu Gideon, kotu ta tattara shaidu da hujjoji da dama da aka gabatar a gabanta, tun bayan fara sauraronta, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

Kotu za ta sanya ranar yanke hukunci kan sojojin da suka kashe Sheikh Goni Aisami
Marigayi Sheikh Goni Aisami da sojoji suka halaka Hoto: Sheikh Goni Aisami Foundation
Asali: Facebook

Ana zargin sojojin da halaka Sheikh Aisami

Kofur John Gabriel ya kashe marigayi Imam Goni Aisami ne a ranar 19 ga watan Agustan 2022, a hanyar Gashua, da bindigarsa ƙirar AK-47, sannan ya gayyaci abokinsa, Adamu Gabriel domin ya taimaka masa wajen jawo motar marigayin ƙirar Honda Accord, wacce ya ce ta lalace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin biyu, Barr. A.S Mohammed, lauyan gwamnatin jihar mai shigar da ƙara da kuma Barr. D.M wanda ke kare wanda ake ƙara, sun yi muhawararsu ta ƙarshe a jiya Laraba, 18 ga watan Oktoba.

Alkalin kotun ya tambayi Kofur John Gabriel ko yana da ja kan tuhumar da ake masa, amma sai ya amsa laifinsa kuma ya yi nadamar aikata laifin kashe fitaccen malamin addinin musuluncin.

Yaushe kotun za ta yanke hukunci?

Alƙalin kotun, mai shari’a Usman Zanna Mohammed, bayan ya duba dukkan hujjoji da bayanan da ɓangarorin suka gabatar, ya ɗage zaman kotun domin yanke hukunci na ƙarshe.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Ƙaramar Hukuma 1 a Jihar Kano, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu da Yawa

A cewar alkalin, za a sanar da ranar yanke hukunci ga ɓangarorin biyu.

An Kori Sojoji Biyu Kan Kisan Sheikh Aisami

A baya rahoto ya zo cewa hukumar sojojin Najeriya ta sallami sojojinta guda biyu da ake zargi da halaka sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami a jihar Yobe.

Hukumar sojin ta ɗauki wannan matakin ne bayan kwamitin bincike da aka kafa ya same su da aikata laifin halaka malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng