Kaduna: Dakarun Sojoji Sun Halaka Miyagun Yan Ta'adda 3
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda uku a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar Kaduna
- Sojojin sun fafata da ƴan ta'addan ne a yankin Udowa na ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- A yayin artabun dai, ƴan ta'adda da dama sun tsere yayin da sojojin suka samu nasarar ƙwato makamai masu yawa a hannunsu
Jihar Kaduna - Aƙalla ƴan ta'adda uku ne dakarun sojojin Najeriya suka kashe a yankin Udowa na ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Dakarun sojojin dai sun fita aikin kakkaɓe miyagun ƴan ta'adda da ke aikata ayyukan ta'addanci a yankin.
Hakan na zuwa ne biyo bayan umarnin da babban hafsan soji ya bayar na fatattakar ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan.
"Furuci Na Kishin Kasa": Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan LP Ta Ce Yan Majalisunta Su Ki Karbar Motocin N160m
Yadda aka sheƙe ƴan ta'addan
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce dakarun Bataliya ta 2, a yayin da suka samu bayanin sirri a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, sun yi wa ƴan ta'adda kwanton ɓauna, inda aka kashe uku daga cikinsu bayan musayar wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Birgediya-Janar Nwachukwu, yayin da yake nuna hotunan ƴan ta'addan da aka kashe ga manema labarai a Abuja, ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin sojojin da suka yi arangamar ya rasa ransa.
A kalamansa:
"A yayin farmakin sojojin sun halaka ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya guda uku a wani ƙazamin musayar wuta, yayin da wasu suka ranta a na kare."
"Sojoji sun samu nasarar ƙwato daga hannun ƴan ta'addan da suka tsere, harsasai 111 masu kaurin 7.62mm, AK-47 guda ɗaya, babura guda biyu, rediyon sadarwa mai ƙarfin gaske da kuma wayoyin hannu guda biyu. Abin baƙin ciki shine, soja ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar."
Yan Bindiga Sun Sace Hakimi
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Bagega a ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum uku tare da yin awon gaba da Hakimin ƙauyen, ɗiyarsa da wasu mutane masu yawa.
Asali: Legit.ng