Sojin Najeriya Sun Kubutar da Mutane 17 Daga Hannun ’Yan Bindiga a Jihar Kebbi

Sojin Najeriya Sun Kubutar da Mutane 17 Daga Hannun ’Yan Bindiga a Jihar Kebbi

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kubutar da wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi
  • Kakakin rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa
  • Ya bayyana cewa samun nasarar bai rasa nasaba da irin taimakon da su ke samu daga mutane kan ba su bayanan sirri

Jihar Kebbi – Rundunar soji na ‘Operation Hadarin Daji’ ta yi nasarar kwato wadanda aka yi garkuwa da su mutum 17 a jihar Kebbi.

Rundunar ta kuma kwato Babura daga hannun ‘yan ta’adda da su ke amfani da su wurin aikata laifuka.

Sojoji sun ceto mutane 17 daga masu garkuwa a jihar Kebbi
Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar da Mutane 17 a Kebbi. Hoto: VOA.
Asali: Facebook

Yaushe aka ceto mutanen daga masu garkuwa a Kebbi?

Kakakin rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoba a cikin wata sanarwa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Mu 100 Mu Ka Auka Makaranta, Aka Yi Awon Gaba da Yara a 2021 – ‘Dan Bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri daga al’umma bayan sace mutanen a kauyen Kanye da ke karamar hukumar Danko-Wasagu da ke jihar.

Sanarwar t ace:

“Rundunarmu ta kai farmakin bazata kan wasu ‘yan ta’adda a kauyen Karenbana inda su ka tsere tare da barin wadanda su ka sacen.
“Hakan ya yi sanadin tserewarsu da raunuka na harbin harsasai inda mu ka kwato wadanda aka yi garkuwa da su guda 17.
“Daga cikin wadanda aka ceto din akwai mata shida da kuma maza 11 wadanda aka sace a karamar hukumar Danko-Wasagu da ke jihar Kebbi.”

Wane sako kwamnadan sojin ya tura wa dakaru?

Sanarwar ta kara da cewa an damka wadanda aka ceton ga shugaban ‘yan sanda na yankin a Bena don hada su da iyalansu, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Kashe 'Yar Kishiyarta Kan Bata Jikinta Da Kashi, Ta Yi Martani

Kwamandan rundunar hadin gwiwa, Mejo Janar Godwin Mutkut ya yabawa yadda rundunar ta yi gaggawar ceto mutanen inda ya hore su da su kara kaimi don ci gaba da ceto mutane.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da saka ido da kuma kawo duk wani rahoto da zai taimakawa rundunar don samun zaman lafiya.

Mutane 2 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

A wani labarin, akalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya.

Rikicin ya barke ne a kauyen Kwanga da ke karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel