Darajar Naira: Bayan Alkawarin Gyara Tattalin Arziki, Tinubu Ya Kafa Mafi Munin Tarihi
- Duk da kokarin da sabon Gwamnan bankin CBN yake yi, an gagara rike farashin Dalar Amurka a kasuwar canji a Najeriya
- An canza Dala kan sama da N1, 100 a makon nan, rahotanni sun nuna wannan ne karancin darajar da Naira ta taba yi a tarihi
- Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin zai gyara tattalin arzikin Najeriya, yanzu ya shafe watanni kusan biyar ya na rike da kasar
ABUJA – Kudin Najeriya na Naira ya yi wani mummunan faduwa a kasuwar canji da kafar I & E a tsakiyar makon nan da ake ciki yau.
Rahoto ya zo cewa bayanan da aka samu daga shafin AbokiFX masu tattara farashin kudin kasashe ya nuna Naira ta yi mummunan fadi.
Karancin Dalar Amurka ya jawo farashin kudin kasar wajen ya yi tsadar da ba a taba gani ko aka ji labarinsa a tarihin canji kudi a kasar ba.
Dala ta haura N1, 100 a BDC
A ranar Talata, aka saida kowace Dala a kan N980, zuwa Laraba kuwa abin ya kara tabarbarewa, an canji Dala ne kan sama da N1, 100.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Nairametrics ya ce ‘yan kasuwar canji sun rika cinikin Dala kan N1,100-N1,110.
A kafar I & E da bankin CBN ya fito da shi domin masu shigo da kaya daga kasashen waje, Naira ta karye zuwa N848/$1 a cikin makon nan.
Kamar yadda This Day ta kawo rahoto, an fahimci farashin Dalar Amurkan ya tashi ne daga N1060/$1 zuwa N1100/$1 a cikin awanni 24.
Bankuna sun canza farashi zuwa N848.12/$1 daga N778.80/$1 da su ka saida a ranar Litinin, hakan ya nuna akwai yiwuwar farashin ya tashi.
Babban bankin CBN ya yi alkawarin kawo sauyi, wannan ya sa a makon jiya aka cire takunkumin da aka kakaba a kan wasu kayayyaki 43.
A lokacin yakin neman zabe a APC, Bola Tinubu ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya, zuwa yanzu abubuwa ba su canza ba.
Ana kukan kudi, Majalisa ta na raba motoci
Ana haka ne sai ga rahoto cewa majalisa za ta kashe N40bn a kan motoci, ‘yan Majalisar sun ce ba a kan su aka fara rabon motocin aiki.
Mai magana da yawun ‘yan majalisa ya ce ba kyauta ake ba su motocin nan ba, aro ne kurum kamar yadda ake ba duk wani babban jami'i.
Asali: Legit.ng