Biki Bidiri: Gwamnatin Zamfara Za Ta Aurar Da ‘Yan Mata Marayu

Biki Bidiri: Gwamnatin Zamfara Za Ta Aurar Da ‘Yan Mata Marayu

  • Gwamnatin Zamfara ta gama shirye-shirye tsaf don aurar da yan mata marayu a jihar
  • Hajiya Huriyya Dauda, matar Gwamna Dauda Lawal, ta ce gwamnatin maigidanta za ta dauki nauyin yi wa yan matan kayan daki da duk abubuwan bukata
  • Za a gudanar da bukukuwan yan mata marayun ne a gidajen marayu da ke garin Gusau, babban birnin jihar

Jihar Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta kammala shirye-shirye domin gudanar da shagalin bikin mata marayu da ke zaune a gidajen marayu a garin Gusau, babban birnin jihar.

Uwar gidan gwamnan jihar, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ce ta tabbatar da wannan ci gaban, jaridar Leadership ta rahoto.

Gwamnatin Zamfara za ta aurar da yan mata marayu
Biki Bidiri: Gwamnatin Zamfara Za Ta Aurar Da ‘Yan Mata Marayu Hoto: @Kdankasa
Asali: Facebook

Mai ba uwargidar gwamnan shawara ta musamman kan harkokin labarai, Zara’u Musau ce ta sanar da hakan ga manema labarai a garin Gusau.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Za mu samarwa amaren duk abubuwan da iyaye za su yi masu, uwargidar gwamnan Zamfara

Zahra'u ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hajiya Huriyya Dauda ta ziyarci gidan marayu da ke garin Gusau, ta jadadda bayar da kulawa da tarbiyya da walwala ga marayu a jihar.
“Uwar marayun ta kara da cewa gwamnatin Zamfara, karkashin jagorancin mijinta za ta yi iya bakin kokarinta wajen sauke nauyin yi masu auren, da abubuwan da amare ke bukata daga iyaye da yardar Allah za mu samar musu da shi in sha Allah."

Hajiya Huriyya ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kara yin addu’o’in zaman lafiya a jihar tare da samun nasara a ayyukan da gwamnatin ta sa a gaba.

Har ila yau, kwamishinar harkokin mata dakanan yara da walwalar al'umma ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, ta ba da tabbacin cewa a shirye gwamnatin jihar ta ke ta gudanar bikin auren yan mata marayu a Gusau.

Kara karanta wannan

Isra'ila/Falasdinu: Iran Ta Tura Gargadi Ga Isra'ila Kan Gaza, Ta Bayyana Matsayarta

Kano: Yan sanda sun kama mutum 30 kan yunkurin tayar da tarzoma yayin auren gata

A wani labarin kuma, mun ji cewa bayanai sun nuna akalla mutane 30 ne suka shiga hannu bisa zargin yunƙurin tada zaune tsaye yayin bikin 'Auren Gata' da aka yi kwanan nan a jihar Kano.

A ranar Jumu'a da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin haɗa ma'aurata 1,800 a faɗin kananan hukumomin jihar guda 44, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng