'Ka Da Ka Kira Sunana a Misalinka', Akpabio Ga Shugaban EFCC

'Ka Da Ka Kira Sunana a Misalinka', Akpabio Ga Shugaban EFCC

  • Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a roki shugaban hukumar EFCC ya cire sunansa a misalin da ya ke yi na yakar cin hanci
  • Wannan na zuwa bayan Olu Olukoyede ya kira sunan Akpabio yayin da ya ke jawabi a majalisar lokacin tantance shi a Abuja
  • Akpabio daga bisani ya roke shi da ya cire sunansa a misalin inda ya ce ya yi duba zuwa wurin zaman mambobin adawa da ke majalisar

FCT, Abuja – An samu wata ‘yar muhawara da ta zama raha bayan shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi shugaban EFCC, Ola Olukoyede kan yin misali da shi.

Akpabio ya bayyana haka ne bayan Olukoyede na misali da shi kan yaki da cin hanci a kasar yayin da ake tantance shi a majalisar.

Kara karanta wannan

Wayyo ‘Yan Bindiga Za Su Karasa Mu – ‘Dan Majalisa Ya Kai Kuka Wajen Gwamnati

Akpabio ya roki shugaban EFCC ya cire sunansa a misalin yaki da cin hanci
Akpabio ya fada wa shugaban EFCC ya cire sunansa a misalin da ya ke. Hoto: Godswill Akpabio.
Asali: Facebook

Meye shugaban EFCC ya ce wa Akpabio?

Olukoyede ya bayyana a dakin majalisar a yau Laraba don tantance shi inda ya kira sunan Akpabio yayin da ya ke ba da misalin yadda za su yaki cin hanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani ya yi birki bayan ya fahimci majalisar ba ta ji dadin hakan ba yayin da kuma su ka barke da dariya, Daily Trust ta tattaro.

Ola ya ce:

“Idan mu na binciken shugaban majalisar Dattawa misali…in ji Olukoyede inda a lokacin mambobin majalisar su ka barke da dariya.

A wannan lokacin ne Akpabio ya roki Ola da kada ya yi amfani da sunansa a matsayin misali yayin da mambobin su ka sake fashe wa da dariya, Daily Post ta tattaro.

Meye Akpabio ya ce kan shugaban EFCC?

Akpabio ya ce:

Kara karanta wannan

Rigima Aka Yi? Gaskiya Ta Bayyana Kan Abin da Ya Jawo Sanatan APC Ya Fice Daga Zauren Majalisar Dattawa

“Ina murna da cewa wanda mu ke tantancewa ya na amfani da sunana a matsayin misali, amma ka cire sunan shugaban majalisar a ciki a yanzu, ka yi duba can wurin (ya na nuna inda ‘yan adawa su ka zaune).”

Olukoyede bayan wannan rahar da aka yi ya ci gaba da jawabi ba tare da kiran sunan kowa ba.

Ya ce:

“Idan kana yakar cin hanci, dole za ka zama abokin gabar kowa musamman a kasa irin Najeriya.”

Majalsa ta tabbatar da nadin shugabannin EFCC, NSIPA

A wani labarin, Majalisar Dattawa ta kamala tantance shugabannin Hukumomin EFCC da NSIPA.

Majalisar ta tabbatar da Ola Olukoyede da Halima Shehu a matsayin shugabannin hukumomin EFCC da NSIPA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.