Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Tallafin Kudi Ga Gidaje Miliyan 15
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15 domin rage musu raɗaɗi
- Sabon shirin rabon tallafin kuɗaɗen dai zai amfani ƴan Najeriya miliyan 62 waɗanda ke fama da matsanancin talauci
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume shi ne ya wakilci Shugaba Tinubu wajen ƙaddamar da shirin da aka yi a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15.
Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa taron ƙaddamar da shirin ya gudana ne a ɗakin taro na ƴan jarida na gidan gwamnati da ke Abuja, a ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, shi ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen taron wanda ya zo daidai da ranar yaƙi da fatara ta duniya.
Tinubu ya sanar da shirin bayar da tallafin kuɗin ne a lokacin da ya gabatar da jawabin ranar samun ƴancin kai ga ƴan Najeriya a ranar 1 ga Oktoban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Najeriya nawa ne za su amfana?
Ministar agaji da kawar da talauci, Betta Edu, ta ce gidaje miliyan 15 ɗin suna wakiltar ƴan Najeriya miliyan 62.
A cewar Edu, Naira 25,000 za a riƙa ba wadanda suka amfana da shirin a kowane wata har na tsawon watanni uku, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Ministan ta ƙara da cewa za a kaddamar da wani sabon shiri mai suna ‘Iya Loja Funds’ domin bayar da lamuni mai sauƙi na N50,000 domin tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa.
A wajen rabon kuɗin ga waɗanda za su amfana da shirin, ministan kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa za a samar da tsarin tantance wa na amfani da bayana ƴan yatsu domin tabbatar da gaskiya da bin diddigi.
Sabon Tallafin Tinubu Ga Dalibai
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tallafi ga ɗaliban Najeriya da ke karatu a makarantun gaba da sakandare.
Shugaban ƙasar ya bada umarnin raba motocin Bas-Bas ga jami'o'i, kwalejojin fasa da kwalin ilimin da ke sassan ƙasar nan baki ɗaya, domin sauƙaƙawa ɗalibai wajen zirga-zirga.
Asali: Legit.ng