'Tufafin N470,000 Na Siya Da Kudin Fansar Da Na Karba', Dan Bindiga Da Yan Sanda Suka Kama a Adamawa

'Tufafin N470,000 Na Siya Da Kudin Fansar Da Na Karba', Dan Bindiga Da Yan Sanda Suka Kama a Adamawa

  • Daya daga cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Adamawa ya bayyana yadda ya kashe kudaden kudin fansa da ya karba
  • Gaiya Usman ya bayyana wa jami'an ‘yan sanda cewa ya karbi Naira dubu 470 rabonsa wanda ya yi amfani da su wurin siyan kayan sakawa
  • Ya bayyana cewa sun karbi kudin fansa Naira miliyan takwas daga iyalan wadanda su ka kaman a karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa

Jihar Adamawa – Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta kama wani matashi mai shekaru 25 kan zargin garkuwa da mutane.

Wanda ake zargin mai suna Gaiya Mallam Usman ya ce ya yi amfani da kudin fansa har Naira dubu 470 don siyan kayan sakawa.

'Yan sanda sun cafke matashin mai garkuwa da mutane a jihar Adamawa
Yan Sanda Sun Cafke Matashi Kan Zargin Garkuwa da Mutane. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye ake zargin matashin da aikatawa a Adamawa?

Gaiya da wasu mutane guda hudu wadanda su ka tsere sun yi garkuwa da wasu mutane uku a karamar hukumar Girei ta jihar inda su ka karbi Naira miliyan takwas.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Bulala 15 Saboda Satar Rake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ake binciken Gaiya, ya bayyana cewa ya karbi Naira dubu 470 a matsayin rabonsa daga cikin miliyan takwas inda ya ce duk kayan sakawa ya siya da su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Suleiman Nguroje ya ce Usman da abokan aikinsa sun yi nasarar yin garkuwa da mutane har sau uku, Daily Trust ta tattaro.

Wane martani rundunar 'yan sanda ta yi a Adamawa?

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Afolabi Babatola ya umarci sashin bincike da su gudananr da kwakkwaran bincike don hukunta wanda ake zargi.

A jihar Adamawan har ila yau, wata mata mai suna Zuwaira Yusuf ta shaki iskar ‘yanci bayan shafe watanni takwas a gidan kaso kan satar riga da kular abinci.

Kotun majistare da ke Gombi ta daure matar tsawon shekaru 2 bayan kama ta da laifin sata wacce ta kasance a daure bayan yanke hukuncin, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kano

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Yola da ke karamar hukumar Karaye a cikin jihar Kano.

Maharan sun kai harin ne inda su ka sace mutane da dama wadanda har zuwa hada wannan rahoto ba a tantance yawansu ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya afku ne bayan hare-haren da maharan su ka kai kauyen a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.