Gwamna Zulum Ya Ba ‘Yan Mata Awanni 12, Zai Rugurguza Gidajen Lalata a Jihar Borno
- Babagana Umara Zulum ya samu labarin abubuwa masha’a da bata-gari su ke aikatawa a yankin ‘Bayan Quarters’ a birnin Maiduguri
- Gwamnan jihar Borno ya yi tir da yadda filin da gwamnati ta ba NRC ya koma mafakar ‘yan kwaya, shaye-shaye, daba da matan banza
- A wata sanarwa dazu, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba kowa awa 12 ya bar Bayan Quarters, za a ruguza gidajen a cikin makon nan
Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada umarni a rusa duk wasu gidajen matan banza da mafakar miyagun ‘yan daba.
A ranar Talata, Mai girma Gwamnan ya fitar da jawabi a shafinsa na Facebook, ya na mai sanar da wannan mataki bayan ya ganewa idanunsa.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci wata unguwa da ake kira ‘Bayan Quarters’ a bayan rukunin gidajen ma’aikatan hukumar jirgin kasa.
Zulum ya ce 'yan iskan gari su na barna
A wannan yanki da ke garin Maiduguri, Gwamnan ya ce ‘yan daba, ‘yan kwaya, mata masu zaman banza da sauran bata-gari duk su ke fakewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce akwai matan da ke zaman banza wanda ya sabawa doka, saboda haka gwamnatin jihar Borno ta dauki mataki game da su.
Gwamna Babagana Zulum ya koka kan yadda ake samun karuwar laifuffuka wanda su ke zama barazana ga gwamnati da daukacin al’umma.
A cewar Farfesa Zulum, irin wannan aika-aika su na zubar da kima da darajar masu yin su.
Farfesa Zulum ya tsaida wa'adi
Ganin yadda wurin ya zama mafaka ga kananan ‘yan mata da mata masu lalata, za a rusa gidajen nan da awanni 72, wa’adin kwanaki uku kenan.
Ana bukatar duk wanda ya ke zama a wadannan gidaje da su ka saba doka, su tashi nan da awanni 12, tashar Channels TV ta tabbatar da haka.
“An sanar da gwamnati a kan ta’asar da ake yi a nan, wannan wuri ya sabawa doka. Ana kashe mutane a nan, wurin ya zama mafakar ‘yan ta’adda.
Saboda haka na bada umarnin kowa ya tashi ya bar wurin nan."
- Babagana Umara Zulum
Asali gwamnatin Jihar Borno ta bada filin ne ga hukumar NRC, amma sai ta bada haya ga masu barna, yanzu Zulum ya karbe takardun filin.
Kokarin gwamnatin Kano
Labari ya zo cewa Gwamnatin Kwankwasiyya ta kashe N1.3bn wajen biyawa mutum 57, 000 kudin jarrabawowin NECO da kuma NBTE a jihar Kano.
A makon nan za a fara aika yara karatu zuwa ketare kuma an bada kyautar kayan makaranta iri-iri ga daliban da su ke makarantun gwamnati.
Asali: Legit.ng