Abba Zai Tura Yara 1001 Zuwa Kasar Waje Bayan Ya Rabawa Dalibai Kayan Makaranta

Abba Zai Tura Yara 1001 Zuwa Kasar Waje Bayan Ya Rabawa Dalibai Kayan Makaranta

  • Mai girma Abba Kabir Yusuf zai dauki nauyin karatun wasu Kanawa a jami’o’in kasar Indiya domin su zurfafa karatun boko
  • Gwamnatin Kano ta kuma raba kayan makaranta, litattafai, da na’urorin zamani ga yaran da ke makarantun gwamnatin jihar
  • Baya ga haka, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biyawa dalibai 57, 000 kudin jarrabawar gama sakandare na NECO da NBTE

Kano - A makon nan ake sa rai gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf za ta tura yara karatu zuwa ketare.

Malam Ibrahim Adam wanda ya na cikin hadiman jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida haka a shafin Facebook.

Idan abubuwa sun tafi yadda ake so, a ranar Juma’a, 20 ga Oktoba 2023, za a kaddamar da shirin kai yara jami’o’in kasan waje.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Yi Bindiga da Naira Miliyan 400 a Kan Otel a Taron UN a Amurka

Abba a Kano
Gwamnan Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

'Yan Kano za su tafi karatu a Indiya

Sahun farko na wadanda aka zaba za su tafi jami’o’in Sharda, Swarnnim da kuma S & R da ke kasar Indiya domin su karo ilmin zamani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin kaddamar da gagarumin shirin zai zo daidai da lokacin da ake murnar cikar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 a Duniya.

Abba ya biya kudin jarrabawa a Kano

Ana haka sai ga rahoto daga Daily Nigerian cewa gwamnatin Jihar Kano ta kashe N1.3bn wajen biyan kudin jarrabawowin NECO da NBTE.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biyawa ‘yan asalin Kano 57,000 kudin rubuta jarrabawar, an sanar da haka lokacin rabon kayan karatu.

Gwamna Abba ya raba kayan karatu

A yunkurin ganin an bunkasa sha’anin ilmi a Kano, Mai girma Abba Kabir-Yusuf ya yi rabon littatafai da kayan karatu ga daliban firamare.

Kara karanta wannan

Manya-Manyan Malaman Musulunci 5 da Su Ka Halarci Walimar Auren Gata a Kano

Gwamnan ya ce nan gaba gwamnatin Kano za ta fara biyan N20, 000 ga ‘yan mata marasa karfi 40, 000 domin su iya kammala karatun boko.

Abba Gida Gida ya ce za su gina makarantu domin rage adadin yaran da ba su karatu. Hakan ya na zuwa ne bayan aurar da mutane kusan 2000.

A karshe, an ware kudi kimanin Naira miliyan 450 domin a dauki jami’an BESDA aiki. Za a dauki aikin ne bayan an tantance ma’aikatan.

Hisbah ta aurar da mutane a Kano

A makon jiya ne rahoto ya cika ko ina cewa Shugaban Hisbah, Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci aurar da mata da gwamnatin Kano ta yi.

Manyan malaman addini irinsu Muhammad Sani Yahaya Jingir, Muhammad Kabir Gombe da Sani Shariff Bichi sun je wajen walimar auren gatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel