Yadda Kotun Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Bulala 15 Kan Satar Rake

Yadda Kotun Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Bulala 15 Kan Satar Rake

  • Wani matashi mai suna Yakubu Haruna ya gurfana a gaban wata kotun musulunci mai zama a Kwana Hudu na jihar Kano
  • An dai kama Haruna da laifin satar rake sanda biyu bayan Abdullahi Muhammad ya yi kararsa ofishin yan sanda
  • Bayan amsa laifin da ya yi, Khadi na kotun, Mai shari'a Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin bulala 15 kasancewarsa sabon shiga a harkar

Jihar Kano - Wata kotun shari'a da ke zama a Kwana Hudu a jihar Kano ta yi umurnin yi wa wani matashi dan shekaru 25, Yakubu Haruna, bulala 15 saboda satar rake.

Da farko, mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya fada ma kotun cewa wani Abdullahi Muhammad, mazaunin Rimin Kebe, ya yi kai wa yan sanda a Zango kara cewa wanda ake karar ya sace masa sandar rake guda biyu.

Kara karanta wannan

Kano: An Kama Mutum 30 Kan Yunkurin 'Tayar da Tarzoma' a Wurin Auren Gata 1,800, Sun Yi Bayani

A cewarsa, hakan ya ci karo da sashi na 133 na dokar Penal Code na jihar Kano.

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala 15
Yadda Kotun Kano Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Bulala 15 Kan Satar Rake Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake yi masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kan haka ne Khadi na kotun, Nura Yusuf Ahmed, ya yi umurnin cewa a yi masa bulala 15 kasancewar wannan ne karo na farko da yake aikata laifin.

Yan sanda sun damke wani matashi kan satar shinkafa buhu 47 a jihar Ogun

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa wata kotun shari'a da ke zamanta a karamar hukumar Kura na jihar Kano ta bada umurnin a yi wa wani Ibrahim Musa Tofa, bulala 10 saboda satar rake daga wani gona.

Wani Malam Ibrahim Isah Usman ne ya yi karar Tofa a kotu bayan mai gonar ya kama shi da taimakon wasu leburori saboda kutse cikin gonarsa cikin dare tare da sace rake.

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

An tasa keyar matashi zuwa gidan kaso shekaru 10 a Kano kan safarar tabar wiwi

A wani labarin kuma, babbar kotun Tarayya da ke Kano ta daure wani Mohammed Bako Sambo daurin shekaru 10 a gidan kaso kan zargin safarar kwayoyi da tabar wiwi.

Hukumar NDLEA a jihar Kano ta gurfanar da Sambo da wasu mutum bakwai a gaban Mai Shari'a, S. A Amobeda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng