Ku Yi Dokar da Zata Tilasta Wa Ma'aikatan Gwamnati Kara Aure, Malami Ga Majalisar Jigawa

Ku Yi Dokar da Zata Tilasta Wa Ma'aikatan Gwamnati Kara Aure, Malami Ga Majalisar Jigawa

  • Sheikh Aminu Waziri ya yi kira ga majalisar dokoki ta yi dokar da zata wajabta wa ma'aikatan gwamnati ƙara aure fiye da ɗaya
  • Shehin Malamin ya ce ya kamata duk ma'aikacin da ya haura mataki na 12 a Albashi ya ƙaro aure saboda mata sun yi yawa
  • A cewarsa, Alqur'ani mai girma da Sunnah sun yi bayani kan kima da darajar aure a wurin Allah

Jihar Jigawa - Fitaccen Malamin addinin islama, Sheikh Aminu Baba Waziri, ya buƙaci mambobin majalisar dokoki su kirkiro dokar da zata tilasta wa ma'aikatan gwamnati ƙara aure.

Shahararren Malamin ya yi wannan kiran ne a wani wa'azi da ya yi a masallacin kasuwanci na Takur da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sheikh Waziri ya aike da saƙo ga majalisa.
Ku Yi Doka Da ZaTa Tilasta Wa Ma'aikatan Gwamnati Kara Aure, Malami Ga Majalisar Jigawa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya ƙara da bayanin cewa duba da yawan da mata suka yi a zamanin da ake ciki, ya kamata maza su riƙa taimaka wa suna ƙara aure domin al'umma ta ginu kan tafarki mai kyau.

Kara karanta wannan

Kano: An Kama Mutum 30 Kan Yunkurin 'Tayar da Tarzoma' a Wurin Auren Gata 1,800, Sun Yi Bayani

Sheikh Waziri ya koka kan yadda mata suka yi yawa, zawara wa da 'yan mata kuma suna son yin auren amma ba bu mazan da zasu aure su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata sun yi yawa a yanzu - Sheikh Waziri

A ɗaya bangaren kuma Shehin Malamin ya nuna damuwarsa kan yadda maza ba su son ƙara aure duk da ga mata nan birjik suna dakon waɗan da zasu aure su.

Ya kuma yi bayanin cewa Aure na ɗaya daga cikin ginshiƙai masu muhimmanci a Addinin Musulunci.

Sheikh Waziri ya jaddada cewa Alqur'ani mai tsarki da Sunnar Annabi Muhammad (SAW) sun ja hankali kan muhimmancin aure da kimarsa a wajen Allah.

Da yake kafa Hujja da Alƙur'ani mai girma, Malamin ya ce:

"A Surah ta hudu, aya ta uku, Allah mai girma da ɗaukaka ya ce, "....Ku auri waɗan da kuke so (mata) ɗaya, biyu, uku ko huɗu, idan kuna ganin ba zaku yi adalci a tsakaninsu ba ku auri ɗaya ko kuma abin da ya halatta a gare ku..."

Kara karanta wannan

"Na Shirya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga" Gwamnan Arewa

Amarya Ta Fusata Bayan Angonta Ya Tiki Rawa da Mahaifiyarta

A wani rahoton kuma Wani faifan bidiyon bikin aure ya nuna lokacin da wani ango ya yi rawa da surukarsa a wajen bikin aurensa, kuma da alama amaryarsa ba ta ji daɗi ba.

Da alama matar ta ji cewa mijinta ya yi watsi da ita saboda yadda ya manne da mahaifiyarta, yana riƙe da ƙugunta yayin da suke rawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel