Masu Garkuwa Sun Hallaka Mutum 1 Tare da Raunata Wasu 2 Yayin Farmaki Kan Motar Bas a Benue

Masu Garkuwa Sun Hallaka Mutum 1 Tare da Raunata Wasu 2 Yayin Farmaki Kan Motar Bas a Benue

  • Tashin hankali yayin da masu garkuwa su ka kai farmaki kan wata motar bas a jihar Benue da daren ranar Alhamis
  • Maharan sun kai farmakin ne yayin da su ka fito daga cikin daji inda mutum daya ya rasu yayin da biyu su ka ji rauni
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Catherine Anene ta tabbatar cewa daya daga cikin mutane ukun ya rasu a asibiti

Jihar Benue – Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wata motar bas ta gwamnati da ke dauke da fasinjoji a kan hanyar Naka da ke jihar Benue.

Shaidun gani da ido sun tabbatar cewa motar na cikin tafiya ne kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo yayin da ‘yan bindigan su ka kai musu harin.

'Yan bindiga sun yi ajalin mutum 1 tare da raunata wasu 2 yayin harin motar bas a Benue
Masu Garkuwa Sun Hallaka Mutum 1 Tare da Raunata 2 a Benue. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Mutane nawa su ka mutu a harin na Benue?

Kara karanta wannan

Ana Cikin Murna Yayin da Sojin Najeriya Su Ka Yi Barin Wuta Kan Masu Garkuwa Tare Da Ceto Mutane 17

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru a ne a daren Alhamis 12 ga watan Oktoba inda harin ya yi sanadin mutuwar mutum daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hari ya kara tayar wa mutane hankali yayin da a kwanakin nan ake yawan kai wa motocin bas na ‘Benue Links’ farmaki tare da garkuwa da mutane.

A kwanakin an kai farmaki tare da hallaka mutane uku yayin da fasinjoji da dama ke hannun ‘yan bindigan, cewar Trust Radio.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ta tabbatar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu mutane biyu su ka samu raunuka.

Anene ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe takwas na dare a ranar inda ta ce jami’an tsaro sun yi gaggawar isa wurin inda su ka dakile kokarin ajalin mutanen.

Kara karanta wannan

‘Yan Fashi Sun Yi Shigan ‘Yan Sanda, Sun Yi Satar Miliyoyin Kudi Ido Ya Na Ganin Ido

Wane martani 'yan sanda su ka yi kan harin na Benue?

Ta ce:

“Su na tafiya ne a kan hanyar Naka da misalin karfe takwas na dare a ranar Alhamis yayin da ‘yan bindigan su ka far musu daga cikin daji.
“Mutane uku sun ji rauni yayin da ‘yan sanda su ka far musu tare da hana su kasha mutanen uku da su ka yi niyya.
“An kwashe su zuwa asibiti don samun kulawa yayin da daya daga cikinsu ya ce ga garinku a asibitin, ana ci gaba da bincike yanzu haka.”

Anene ta shawarci jama’a da su ci gaba da ba su goyon baya na bayanan sirri don kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Sanatan Benue ya ce iyayensa na sansanin gudun hijira

A wani labarin, Sanata Titus Zam daga jihar Benue ya koka kan yadda har yanzu iyayensa ke sansanin gudun hijira.

Zam ya ce hakan ya faru ne saboda hare-haren 'yan bindiga da ya afku a shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.