Mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Yobe

Mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Yobe

  • Ana cikin jimami yayin da Sanata Ahmed Lawan ya rasa mahaifiyarsa bayan ta riga mu gidan gaskiya a yau
  • Marigayiya Hajiya Halima Ibrahim ta rasu a yau Asabar 14 ga watan Oktoba a garin Gashua da ke jihar Yobe
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi sallar jana’izarta a gobe Lahadi 15 ga watan Oktoba a kofar fadar Sarkin Gashua

Jihar Yobe – An yi babban rashi yayin da mahaifiyar tsohon shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ta riga mu gidan gaskiya.

Marigariya Hajiya Halima Ibrahim ta rasu a yau Asabar 14 ga watan Oktoba a gidanta da ke Gashua a karamar hukumar Bade ta jihar Yobe, Legit ta tattaro.

Mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan ta riga mu gidan gaskiya a Yobe
Mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan Ta Rasu a Jihar Yobe. Hoto: Ahmed Ibrahim Lawan.
Asali: Facebook

Yaushe mahaifiyar Sanata Ahmed Lawan ta rasu?

Hadimin sanatan a bangaren yada labarai, Dakta Ezrel Tabiowo shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yammacin yau Asabar.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Murna Yayin da Sojin Najeriya Su Ka Yi Barin Wuta Kan Masu Garkuwa Tare Da Ceto Mutane 17

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta tabbatar cewa za a binne marigayiyar a gobe Lahadi 15 ga watan Oktoba da misalin karfe 11 na safe a garin Gashua.

Za a gudanar da sallar jama’izar marigayiyar ce a babban masallacin Sarkin garin Gashua da ke kofar Fada kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Meye Ahmed Lawan ya ce kan mutuwar mahaifiyarsa?

Sanarwar ta ce:

“Sanata Ahmed Lawan ya na godiya kan irin sakwannin jajantawa da ya ke samu daga abokai da ‘yan uwa.
“Iyalansa na godewa jama’a da su ke tura musu sakwannin jaje da addu’o’i yayin da da su ke cikin wannan yanayi na bakin ciki.”

Mutane da dama sun tura sakwannin ta'aziyya ga iyalan Sanata Ahmed Lawan wanda tsohon shugaban majlisar Dattawa ne ta tara don jajanta masa irin wannan babban rashi da aka mishi.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar APC Ya Tona Abin da Ya Hana Kawo Karshen Rashin Tsaro a Arewa

Tsohon ministan matasa, Dakta Bello Maitama ya rasu

A wani labarin, Tsohon ministan cikin gida da kuma matasa, Dakta Bello Maitama ya rasu a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoba.

Maitama ya kasance tsohon Sanata wanda ya ba da gudumawa sosai don inganta rayuwar al'ummarshi da ma kasa baki daya.

Marigayin wanda asali dan jihar Jigawa ne ya rasu ne a Kano bayan 'yar gajeriyar jinya da ya yi fama da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.