Rasuwan dattijon arziki, Alh Yusuf Maitama Sule: Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu – Sanata Shehu Sani

Rasuwan dattijon arziki, Alh Yusuf Maitama Sule: Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu – Sanata Shehu Sani

A safiyar yau ne aka samu labarin rasuwan tsohon ministan man fetur kuma dan masanin Kano, Alh Yusuf Maitama Sule. Wannan rasuwa ta girgiza arewacin Najeriya da Najeriya gaba daya.

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi wata jawabi game da irin babban rashin da Najeriya tayi na rasuwar wannan dattijon arzikin.

Yace: “ Rayuwa ta kare. Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu kuma asusun ilimi, hikima, da mutunci. An janye wata labile a wannan mataki na rayuwar kasarmu. Maitama ya kasance masanin tarihi wanda yake sada mu da tarihi domin shiryar da mu domin gobe.

Rasuwan dattijon arziki, Alh Yusuf Maitama Sule: Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu – Sanata Shehu Sani
Rasuwan dattijon arziki, Alh Yusuf Maitama Sule: Munyi rashin babban ginshiki a tarihin kasarmu – Sanata Shehu Sani

Ya kasance wakili na amana, mai mutunci da kuma sadaukar da kai ga kasa. Yayi sadaukar da rayuwarsa ga wasu da kasa. Maitama ya haskaka mu lokacin da muke magagi cikin duhu. Ya kasance mai buga kararrawa akanmu duk lokacin da muka fara batan hanya.

Ya kasance malami wanda muka saurara amma bamu kwaykwaya ba. Ya sadaukar da rabin shekarunsa yana mana bauta, sauran rabin kuma yana karantar da mu.

KU KARANTA: Alh Yusuf Maitama Sule ya rasu

Shine mutumin da yafi kowa dadewa a matsayin ministan man fetur amma bai da rijiyan mai ko gidan mai ko daya. Rayuwan Maitama ya kasance abin koyi ga matasan yanzu. ALLAH ya gafarta masa."

https://www.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel