Shinkafa Da Jerin Abubuwa 43 Da CBN Ya Halatta Karbar Daloli Domin Shigo Da Su
- Babban bankin CBN ya janye haramcin bada kudin kasashen waje domin shigo da wasu kayayyaki 43 da aka kayyade a 2015
- Haramcin ya shafi kayan da ake da su a Najeriya da wadanda gwamnatin baya ta ke ganin cewa babu bukatar a rika shigo da su
- Haramcin ya shafi karbar Daloli da nufin a sayo tumatur, masara, ganye, man gyada ko takin zamani daga kasashen ketare
Abuja - A makon nan ne Babban bankin CBN ya cire takunkumin da ya kakaba wajen shigo da wasu kayayyaki tun shekarar 2015.
Sanarwar da babban bankin ya fitar ta bakin Dr. Isa Abdulmumin a shafukansa a ranar Alhamis ya yi bayanin matakin da aka dauka.
Rahoton nan ya tattaro jerin duka sunayen wadannan kayayyaki da yanzu ya halatta ‘dan kasuwa ya samu kudi domin ya shigo da su.
Bankin CBN na kokarin hana Dala tashi
Kafin yanzu, The Cable ta ce masu bukatar sayo wadannan kaya daga kasashen ketare, su na neman kudi ne da tsada a kasuwar canji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CBN ya yi hakan ne domin yunkurin tallafawa kamfanonin gida da su ke samar da wadannan kaya da kuma tsare mutuncin Naira.
Ga jerin kayan nan kamar haka:
Kayan da CBN ya cirewa takunkumi
1. Shinkafa
2. Siminti
3. Bota
4. Kayan man gyada, man ja da sauransu
5. Nama da kayan nama
6. Ganye da sauran kayan ganye
7. Kaji, kwai, zabi
8. Jiragen sama/jiragen yawo
9. Turaren wutan Indiya
10. Kifin gwangwani
11. Nadadden rodi
12. Shafaffen rodi
13. Kwanon gini
14. Baro
15. Kwanon daukar kaya
16. Akwatin karfe da garwa
17. Kayan tangaran
18. Gangunan karfe
19. Bututun rodi
20. Wayoyin rodi
21. Rodi
22. Karfen waya
23. Kusoshi
24. Wayar tsaro
25. Allon katako
26. Faifen allo
27. Filai wood
28. Kofofin katako
29. Kayan jeren gida
30. Tsinken sakace
31. Gilas
32. Kayan girki
33. Kayan tebura
34. Tayil
35. Tufafi
36. Kayan auduga
37. Yadi/shaddoji/leshi da saurasu
38. Robobi da kayan roba
39. Sabulu da kayan kwalliya
40. Tumatur da tumaturin leda (ko gwangwani)
41. Sayen kudin kasar waje/hannun shari/da sauransu
42. Masara
43. Takin zamani
Masana sun ba Najeriya shawarwari
Ana da labari masanan hukumar IMF da bankin Duniyasun fadawa Bola Ahmad Tinubu da bankin CBN yadda za a samu saukin al’amura
‘Yan kasuwar canji da aka fi sani da BDC su na saida duk Dalar Amurka a kan kusan N1030, an bukaci a kara darajar ruwa wajen bada bashi.
Asali: Legit.ng