EFCC: A Karshe Abdulrasheed Bawa Ya Yi Murabus Yayin da Tinubu Ya Sanar Da Sabon Shugaba
- An rahoto cewa dakataccen shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yi murabus daga matsayinsa
- An sanar da batun murabus din Bawa ne a cikin wata sanarwa da ke sanar da nadin sabon shugaban EFCC, Ola Olukoyede
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Bawa a ranar 14 ga watan Yuni, kuma nan take jami'an DSS suka kama shi tare da tsare shi
Rahotanni sun kawo cewa Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ya yi murabus daga matsayinsa.
Fadar shugaban kasa ce ta sanar da murabus din Bawa a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.
Tinubu ya nada sabon shugaban EFCC bayan Bawa ya yi murabus
A cikin sanarwar, Ngelale ya sanar da nadin Ola Olukoyede da Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sabon shugaba da sakataren hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani bangare na sanarwar ta ce:
"An nada Mista Olukoyede biyo bayan murabus din dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Mista Abdulrasheed Bawa."
Dalilin da yasa SSS suka kama Bawa, dakataccen shugaban EFCC
A ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, sannan rundunar tsaron SSS ta kama shi tare da tsare shi ba tare da wata sanarwa kan kamun nasa ba.
An yi zargin cewa hukumar SSS ta kama Bawa ne bisa umurnin shugaban kasa Bola Tinubu, sannan har zuwa lokacin da aka nada sabon shugaban EFCC, rundunar tsaron farin kayar bata yi bayani kan laifinsa ba da kuma dokar da ta basu izinin tsare shi na tsawon lokaci ba tare da gurfanar da shi ba.
Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada Bawa bayan dakatar da Ibrahim Magu, tsohon shugaban hukumar wanda ake zargin ya samu matsala da atoni janar na tarayya, Abubakar Malami.
Ga sanarwar a kasa:
Tinubu ya nada Olukoyede sabon shugaban hukumar EFCC
Legit Hausa ta kawo a baya cewa shugaba Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) bawan dakatar da Abdulraheed Bawa a matsayin shugaban EFCC.
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba a Abuja, Legit ta tattaro.
A cikin sanarwar, Ngelale ya ce an nada Ola Olukoyede wanda lauya ne a matsayin sabon shugaban hukumar.
Asali: Legit.ng