“Ba Ma Fada”: Kawaye Biyu Da Ke Soyayya Da Saurayi Daya Sun Yada Bidiyonsu a Gado
- Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wani mutum da ke soyayya da wasu kawaye biyu
- An gano su uku kwance suna sharholiya a bidiyo, lamarin da ya ja mutane suka yi masu caaa a kai
- Wasu mutane na tunanin yan matan na tare da mutumin ne saboda kudinsa, yayin da wasu suka yi martani kan yanayin jikinsu
Yan Najeriya sun yi martani a kan wani bidiyo da ke nuna wani mutum da ke soyayya da kawaye biyu a lokaci guda.
Wani shafin Instagram, @naijaeverything, ya yada bidiyon a dandalin soshiyal midiya, inda ya kara da cewar yan matan ba sa fada da junansu.
Shafin ya kara da cewar yan matan sun nuna cewa yana da kyau ka so wa dan uwanka abun da kake so wa kanka.
“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu
"Ah ah!! kawaye 2 suna da saurayi daya kuma ba sa fada. Yau na tabbatar da cewa ka so wa dan uwanka abun da kake so wa kanka," @naijaeverything ya rubuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, yan matan biyu sun sumbaci labban mutumin yayin da suke sharholiya a kan gadon.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
moni.solab ta ce:
"Idan dai har gayen ya siya masu gashin kanti su dukka biyun...ba za a samu sabani ba."
elenna__.sz ta ce:
"Yana da kyau ka so wa dan uwanka abun da kake so wa kanka amma akwai zaman lafiya a cikin samun na kanka."
olasumbo_goldinteriors ta ce:
"Wasu da suka fito gidan kishiyoyi za su dunga zaginsu."
ke___lv1 ta ce:
"Ya Allah gani nan kuma ina sake gode maka da baka bari wani dan uwana ya kunyatani ba a soshiyal midiya. Ina kaunarka Yesu."
wizdomgrams ya ce:
"Ku rabu da shi....da zaran kudi ya kare, idonsa zai bude."
Dan Najeriya zai auri mata biyu a rana daya
A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya Mai suna Prince Okebulu Ndukwo Nkobi, zai yin wuff da tsala-tsalan yan mata biyu a rana daya.
Za a daura auren ne a jihar Abia cikin watan Nuwamba mai kamawa, a harabar gidan iyalin Nkobi da ke garin Abariba a jihar Anambra.
Asali: Legit.ng