CBN Ya Kawo Dauki da Dala Biliyan 5.78 Don Dawo da Martabar Naira a Najeriya
- Babban Bankin CBN, ya bayyana cewa ya kawo dauki don kare darajar Naira da Dala biliyan 5.78
- Bankin ya ce ya dauki wannan matakin ne don tabbatar da tsayuwar Naira da kafafunta a kasuwannin duniya
- Duk da daukin da bankin ya kawo, Naira ta fadi warwas inda ake siyar da ita Naira 1,040 wanda shi ne mafi muni a kwanakin nan
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zuba Dala biliyan 5.78 don kare Naira daga durkushewa a farkon wannan shekara.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce ya sayi fiye da Dala biliyan 655 a kasuwa kamar yadda ya wallafa a sashen yanar gizo na bankin a ranar Talata 10 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.
Meye CBN ya ce kan Farfado da darajar Naira?
Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, bankin ya fadi da kaso 26 na harkokin saye da sayarwa na Dala daga Dala biliyan 7.5.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin ya kawo daukin ne a hada-hadar Dala don samar da su da yawa da kuma tabbatar da tsayawarta.
Duk da wannan dauki da bankin ta kawo, an samu faduwar darajar Naira mafi muni a tarihi a kasuwanni a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba.
Nawa CBN ya ce ake siyar da Naira yanzu a kasuwanni?
Ana siyar da kudin ne kan ko wace Dala kan kudi N1,040 inda ta kara sama da Naira 1,045 a kasuwanni.
Masu fashin baki a harkar tattalin arziki sun yi hasashen cewa Naira za ta iya rugujewa zuwa watan Disamba idan gwamnati ba ta dauki mataki ba.
Masanan na magana ne kan tsare-tsaren da gwamnatin ta kawo na barin Naira ta yi yawo a kasuwa wanda ke kara jawo matsala, cewar Leadership.
NNPC ya ciyo bashin Dala miliyan 3 don farfado da Naira
A wani labarin, kamfanin mai na NNPC ya ce ya karbo bashin Dala miliyan uku don dawo da martabar Naira a Najeriya.
Kamfanin ya ce ya karbo bashin ne a bankin kasar Masar inda ya ce za a na biyan bashin ne da mai.
A kullum darajar Naira kara durkushewa ta ke musamman a kasuwanni idan aka kwatanta da sauran kudaden kasashe masu daraja.
Asali: Legit.ng