Tsohon Minista Hadi Sirika Ya Samu Sabon Mukami a Jihar Katsina

Tsohon Minista Hadi Sirika Ya Samu Sabon Mukami a Jihar Katsina

  • Hadi Sirika tsohon minista a gwamnatin tsohon Shugaba Buhari ya samu muƙami a kwamitin asusun tsaro na jihar Katsina
  • Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya bayyana naɗin nasa cikin kwamitin a wani taron da aka gudanar a jihar a ranar Talata
  • Kwamitin dai zai samar da kuɗaɗen da za su taimaka wa ƙoƙarin gwamnati a yaƙin da take yi da rashin tsaro a jihar

Jihar Katsina - Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya samu sabon muƙami daga gwamnatin jihar Katsina.

Kamar yadda Radio Trust ya ruwaito, an naɗa tsohon ministan ne a matsayin mamba a kwamitin asusun kula da harkokin tsaro na jihar Katsina.

Hadi Sirika ya samu mukami a gwamnatin Katsina
Hadi Sirika ya samu mukami a gwamnatin jihar Katsina Hoto: Hadi Sirika
Asali: Twitter

Katsina ta ƙaddamar da kwamitin asusun tallafawa tsaro na jiha

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 Na Arewa Sun Gana a Katsina, Sun Cimma Matsaya Kan Muhimman Abu 2

An ɗora wa kwamitin alhakin tattara kuɗaɗen da za su taimaka wa ƙoƙarin jihar wajen tunkarar ƙalubalen tsaro a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai sauran jiga-jigan ƴan kasuwa da suke cikin kwamitin waɗanda suka haɗa da Sanata Ibrahim Idah, Alhaji Dahiru Mangal, da Sanata Abu Ibrahim.

Gwamna Dikko Umar Radda a yayin ƙaddamar da kwamitin, ya bayyana cewa sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abdullahi Faskari ne zai jagoranci kwamitin.

Jerin mutanen da ke cikin kwamitin

A cewar Radda, kwamishinonin yaɗa labarai, kuɗi, tsaro da harkokin cikin gida, shugaban ma'aikata na jihar, masu ba da shawara na musamman, da ƴan gudun hijira da kuma waɗanda rikicin ƴan bindiga ya ritsa da su, su ne mambobin kwamitin.

Ya kuma jaddada cewa sauran mambobin sun haɗa da sarakunan Katsina da Daura da kuma shugaban ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya na jihar.

Gwamnan ya buƙaci kwamitin da ya zaƙulo fitattun ƴan asalin jihar da kamfanoni da za su taimaka da tallafin kuɗi tare da ba da shawarar wuraren da ya kamata a tura kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yunƙuro, Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro Domin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Lai Muhammad Ya Sake Samun Mukami

A wani labarin kuma, toshon ministan yaɗa labarai na gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sake samun sabon muƙami mai muhimmanci.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a bangaren yawon bude ido, Zurab Pololikashvili ya naɗa Lai Mohammed a matsayin mai ba shi shawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng