Allahu Akbar: ‘Dan Majalisar Sokoto Ya Rasu Bayan Watanni 4 Ya Na Wakilci

Allahu Akbar: ‘Dan Majalisar Sokoto Ya Rasu Bayan Watanni 4 Ya Na Wakilci

  • ‘Dan siyasa daga jihar Sokoto, Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu ya na kan kujerar majalisar wakilan tarayya
  • Wani abokin aikin ‘dan majalisar ya tabatar da rasuwar jagoran na APC, ya ce yau za ayi jana’izarsa a garin Sokoto
  • Hon. Abdulkadir Jelani Danbuga ya yi jinya a asibiti, wanda cutar tayi sanadiyyar rasuwarsa cikin tsakar daren yau

Abuja - Mai wakiltar mutanen mazabun Isa-Sabon Birni a majalisar wakilan tarayya, Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu a daren yau.

Rahotannin da mu ka samu sun tabbatar da rasuwar Honarabul Abdulkadir Jelani Danbuga da kimanin karfe 12:30 na Larabar nan.

Daily Trust a rahotonta, ta ce ‘dan majalisar tarayyar ya rasu ne bayan ‘yar rashin lafiya.

'Dan Majalisar Wakilan Sokoto
'Dan Majalisar Wakilan Sokoto, Abdulkadir Jelani Danbuga Hoto: Bashiru Gada
Asali: Facebook

Jinyar Abdulkadir Jelani Danbuga a asibiti

A ranar Talata aka kwantar da ‘dan siyasar a asibiti, amma bai wuce awanni 12 ya na jinya a gadon asibitin, sai rai ya yi masa halinsa.

Kara karanta wannan

Jami'an 'Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Kashe 'Yar Kishiyarta Kan Bata Jikinta Da Kashi, Ta Yi Martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulkadir Jelani Danbuga wanda ya na cikin jagororin APC mai mulki ya kasance ‘dan majalisar wakilai tun bayan zaben shekarar nan.

Za a birne 'Dan majalisar a Sokoto

Wata majiya ta shaida cewa za a dauki gawarsa zuwa sabon masallacin da aka gina a majalisa, daga nan sai ayi shirin yi masa jana’iza.

Za a birne ‘dan siyasar ne a mahaifarsa ta Sokoto da kimanin karfe 11:00 na safiyar nan.

Solacebase ta ce ‘dan majalisar Sabon Birni a majalisar dokoki, Aminu Almustapha (Boza), ya tabbatar da rasuwar ‘dan majalisar tarayyar.

Yanzu haka ana ta yi masa addu’ar samun lafiya, rahoton ya ce Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya ‘ya da kuma jikoki.

Abdulkadir Danbuga mai shekara 63 a duniya ya yi takara da kusan mutane bakwai wajen neman takarar kujerar majalisa da ya rasu a kai.

Kara karanta wannan

Sanatoci Na Shirin Karawa Shugaban Kasa Tinubu Karfi a Sabon Yunkuri a Majalisa

Abokan takararsa su ne: Mohammed Saidu, Yakubu Bashir, Sani Sulaimen, Mustapha Adamu, Mamuda Sani, Shehu Abdullahi da Aminu Yahaya.

'Yan siyasar da su ka more a mulki

A jihar Yobe, wani rahotonmu ya nuna yadda Bukar Abba Ibrahim da Ibrahim Gaidam kadai su ka dauki shekaru 20 a kan karagar mulki.

Watakila Sanata Ibrahim Gaidam ne kadai Gwamnan da aka rantsar da shi sau uku a jere. Bayan nan ya zama Sanata kafin a nada shi Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng