Sanatoci Na Wani Shirin Karawa Shugaba Tinubu Karfi a Sabon Yunkuri a Majalisa

Sanatoci Na Wani Shirin Karawa Shugaba Tinubu Karfi a Sabon Yunkuri a Majalisa

  • Kudirin da Opeyemi Bamidele ya gabatar a zauren majalisar dattawa zai rage karfin ma’aikatar jin kai da bada tallafi
  • ‘Yan majalisa su na so tsare-tsaren NSIP su bar karkashin Minista, sai su koma karkashin kulawar shugaban Najeriya
  • Sanatoci irinsu Ali Ndume da Barau Jibrin sun goyi bayan kwaskwarimar da Opeyemi Bamidele ya ke so ayi wa doka

Abuja - Yanzu haka akwai kudirin da aka gabatar a majalisar dattawa domin dauke tsare-tsaren NSIP daga karkashin ma’aikatar tarayya.

The Cable ta ce kudirin ya na so a cire wadannan tsare-tsare daga ma’aikatar jin kai da yaki da talauci, a maida su fadar shugaban kasa.

A ranar Talatar nan, Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar da kudirin a zauren majalisa.

Sanatoci Hoto: Nigerian Senate
Sanata Opeyemi Bamidele a Majalisa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Ina makomar N-Power da sauransu?

Idan ‘dan majalisar na Ekiti ya yi nasara, irinsu N-Power, GEEP, CCT, NHGSFP da Muhammadu Buhari ya kawo, za su bar ma’aikata.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko NSIT ya na karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, daga baya aka kirkiri ma’aikatar musamman.

Bamidele (APC, Ekiti) ya ce kudirin da ya kawo zai taimaka wajen tabbatar da manufar shugaba Bola Tinubu na ganin an yi aiki da gaskiya.

Majalisa za ta yi wa tsarin mulki gyara

Rahoton Premium Times ya ce ‘dan majalisar ya nuna dalilin gyara sashe na 17(3) na kundin tsarin mulki shi ne tabbatar an yi wa kowa adalci.

Kudirin zai yi kwaskwarima ga sashe na 9 (3); 14(1); 21(1); 22(1), 26(1) da na 33 da zai dauke shirin NSIT, ya maida shi fadar shugaban kasa.

Wasu Sanatoci sun yi na'am da kudirin

Jaridar ta ce Sanata Muhammad Ali Ndume (APC, Borno) ya nuna ya na goyon bayan garambawul din, ya ce kyau a amince da kudirin nan.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

Shi ma Sanata Barau Jibrin ya marawa kudirn baya, ya ce hakan zai taimakawa kasar.

Amma Seriake Dickson (PDP, Bayelsa) ya bada shawarar su yi wa abin kallon kurilla, don haka ne Godswill Akpabio ya ce ba za ayi garaje ba.

'Yan majalisar tarayya su na rigima

Ana da labari 'Yan majalisar wakilai sun fadawa Sanatocin Najeriya ba su isa su yi wani nadi a hukumar NDDC ba tare da sa hannunsu ba.

Majalisar dattawa ta tantance wadanda za su zama shugabanni a hukumar Neja-Delta amma daga baya Majalisar wakilai ta ce da sake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng