Ba mu dakatar da shirin Trader Moni ba – Mataimakin Shugaban kasa

Ba mu dakatar da shirin Trader Moni ba – Mataimakin Shugaban kasa

Mun ji labari cewa har gobe tsare-tsaren wannan gwamnati na TraderMoni da kuma Government Enterprise and Empowerment (watau GEEP) su na aiki akasin abin da wasu ke rahotowa na dakatar da su.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya ta tsaida shirin Trader Moni ba gaskiya bane. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi wannan bayani ta bakin babban Hadimin sa.

A wani jawabi da Laolu Akande ya fitar a madadin ofishin mataimakin shugaban kasar, yace har gobe Trader Moni na aiki kuma an samu kananan ‘yan kasuwa har 30, 000 da aka rabawa jari bayan an kammala zaben Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnan APC da aka tsige yace ya daukaka kara a Kotu

Ba mu dakatar da shirin Trader Moni ba – Mataimakin Shugaban kasa
Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo yace Trader Moni na nan
Asali: Twitter

Akande yace an rabawa mutane da dama karin jari na N15000 domin su inganta kasuwancin su. An zabi akalla mutane 30, 000 ne a kowace jiha har ma da Abuja. Yanzu haka dai kusan duk an ci ma wannan buri inji gwamnatin kasar.

Hadimin mataimakin shugaban kasar yace kusan mutane 30, 000 da aka rabawa wannan kudi bayan zabe wannan karo sun fito ne daga jihohohi 10. Wannan ya nuna cewa ba don yakin zabe. Gwamnatin APC ta fito da wannan tsari ba.

Gwamnatin Buhari dai ta sha alwashin cewa za ta bunkasawa ‘yan kasuwa miliyan 10 da kasuwancin su kafin wa’adin ta ya cika. Ana raba bashin jarin N10, 000 ne da ake biya bayan watanni 6, sannan a rika karawa mutum adadin kudin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel