Zaben Nasarawa: Matasan Musulmi Na Arewa Sun Soki Sheikh Mansur Sokoto Kan Wallafarsa a Facebook

Zaben Nasarawa: Matasan Musulmi Na Arewa Sun Soki Sheikh Mansur Sokoto Kan Wallafarsa a Facebook

  • Wata kungiya, Northern Youths Council of Nigeria, ta soki malamin addinin musulunci Sheikh Mansur Sokoto kan rubutunsa da ya janyo cece-kuce a Facebook
  • Malamin ya janyo hankali kan abin da ya kira hatsari ga Musulunci a jihohin Taraba da Nasarawa idan wanda ba musulmi ba ya karbi mulkin jihohin
  • Amma, kungiyar, wacce shugabanta na kasa, Isah Abubakar ya wakilta, ta ja hankalin Sheikh Sokoto da sauran malamai kan furta maganganu da ka iya janyo rashin hadin kai da barazana ga dimokradiyya

Lafiya, Jihar Nasarawa - Wata kungiya mai suna Northern Youths Council of Nigeria, ta soki malamin addinin musulunci Sheikh Mansur Sokoto kan rubutunsa da ya janyo cece-kuce a Facebook.

Legit Hausa ta rahoto cewa Sheikh Sokoto, a wani rubutu a Facebook mai taken "Islam and the North", ya yi ikirarin cewa jihohin Nasarawa da Taraba za su shiga hatsari idan mulki ya fada hannun wanda ba musulmi.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Yi Magana Kan Digirin Tinubu, Ya Fito da Takardun Karatunsa

Matasa Musulmi na Arewa sun ragargadi Sheikh Mansur Sokoto kan
Kungiyar Northern Youth Council ta soki Sheikh Mansur Sokoto kan wallafarsa a Facebook. Hoto: Northern Youths Council of Nigeria
Asali: UGC

"Bitar shari'ar zaben gwamnoni da wasu jihohi cikin yan kwanakin nan abin damuwa ne. Idan Taraba da Nasarawa suka fada hannun wadanda ba musulmi ba, musulunci zai fuskanci hatsari," ya rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ka dena tada zaune tsaye, Kungiya ta fada wa Sheikh Mansur Sokoto

Da ya ta ke martani, kungiyar, cikin sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Isah Abubakar, ta gargadi Sheikh Mansur Sokoto ya guji neman tada rikici ta hanyar shiga harkar siyasa da shari'a.

A cewar Abubakar, irin wannan maganganun "ka iya raba kan yan Najeriya kuma barazana ne ga hukuncin kotu wanda shima barazana ne ga zaman lafiya da dimokradiya."

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"A matsayinmu na musulmi kuma yan arewa, muna mamakin inda Sheikh Sokoto ya samo wannan koyarwar tasa domin musulunci ya koyar da cewa mulki na adalci ya fi muhimmanci kan addinin shugaba.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

"A gare mu, rubutunsa ra'ayinsa kawai da hasashe. Muna son shawartar Sheikh ya mayar da hankali kan yadda zai kawo shawarar kawo karshen yan bindiga da satar shannu da ya zama ruwan dare a jihohin arewa da musulmi ke mulki a matsayin gwamnoni."

"Ka Zama Shugaba, Ba Mai Raba Kan Al'umma Ba", Kungiyar PDP Ta Soki Sheikh Mansur Sokoto

A wani rahoton, kungiyar musulmi yan jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa ta gargadi Sheikh Mansur kan kalamansa da suka janyo cece-kuce.

Kamar yadda Legit Hausa ta rahoto, Mansur Sokoto ya ce musulunci na iya fadawa cikin hatsari idan jihohin Nasarawa da Taraba suka fada hannun wadanda ba musulmi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164