Matar Gwamnan APC Ta Ci Gaba da Ƙoyarwa a Jami'ar Jihar Ekiti

Matar Gwamnan APC Ta Ci Gaba da Ƙoyarwa a Jami'ar Jihar Ekiti

  • Matar gwamnan jihar Ekiti mai ci ta zama abin kwatance yayin da ta koma aji ta ci gaba da karantar da ɗaliban jami'ar EKSU
  • Dokta Olayemi Oyebanji, ta ce zata ci gaba da ware lokaci duk da yawna ayyukan da ke gabanta, ta riƙa karantarwa a jami'ar
  • Uwar gidan gwamnan ta kai matsayin babbar Lakcara a jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo kuma tana gab da zama Farfesa a matakin ilimi

Jihar Ekiti - Uwar gidan gwamnan jihar Ekiti, Dakta Olayemi Oyebanji, ta fara aikin hidimta wa al'umma, inda ta yanke shawarar koyar da dalibai a aji.

Matar gwamnan ta kwashe kimanin awanni biyu tana koya wa daliban kwas ɗin 'Management Education' a Jami’ar Jihar Ekiti (EKSU) domin saka wa al'umma.

Uwar gidan gwamnan jihar Ekiti, Dakta Oyebanji.
Matar Gwamnan APC Ta Ci Gaba da Ƙoyarwa a Jami'ar Jihar Ekiti Hoto: Dr Olayemi Oyebanji
Asali: Facebook

Dakta Olayemi Oyebanji, matar gwamna Biodun Oyebanji na APC a jihar Ekiti ta zuba wa ɗaliban madarar ilimi kuma su kansu ɗaliban sun ji daɗin zama a lakcar da ta yi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Timipre Sylva a Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC a Bayelsa

Shin matar gwamnan ta taɓa koyarwa a jami'a ƙafin yanzu?

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, babbar lakcara ce a jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo, kuma yanzu haka tana dakon a ba ta matsayi na kusa da zama Farfesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinta, matar gwamnan ta ce ta yi farin cikin sake koma wa aji a EKSU inda ta fara aikinta a fannin ilimi kuma ta yi koyarwa na tsawon shekaru 12 kafin ta koma Ibadan.

Ba da daɗewa ba Dakta Oyebanji ta bayyana aniyarta na tsakurar lokaci daga cikin ayyukan da ke gabanta na uwar gidan gwamna domin ta karantar da ɗalibai a jami'a mallakin jihar Ekiti.

Ɗalibai sun ji daɗin lackar Dakta Oyebanji

Ɗaliban sashin koyar da ilimin "Education Management" sun nuna farin cikin su da ganin matar gwamna da kanta ta zo aji tana koyar da su wani Kwas mai taken "Jagoranci a ƙungiyoyin zamani."

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Wata Mata Ɗauke da Kwalayen Kayan Laifi Sama da 50 a Filin Jirgin Sama a Jihar Kano

Yayin lakcar, Dakta Oyebanji ta musu bayani kan ƙa'idojin jagoranci kuma daga ƙarshe ta amsa tambayoyi daga ɗaliban, Guardian ta ruwaito.

Wani malamin jami'a da ke dab da kai wa matakin Dakta, Mansur Salisu, ya faɗa wa Legit Hausa cewa ba shakka matar gwamna ta ciri tuta da har ta iya zuwa ta karantar da ɗalibai.

Ya ce:

"Lallai ta ciri tuta. Wannan shi yake nuna mana tsantsar ƙaunarta da harkar ilimi da cigaban sa, tunda har ta iya ware lokaci domin bada gudunmawa duk da ƙarancin lokaci da kuma ayyukan dake gabanta na Mai-ɗakin gwamna."
"Kuma wannan zai bama ita jami'ar wata dama domin shigar da bukatunta kai tsaye ga gwamna ta hannun Mai-ɗakinsa tunda jami'ar mallakin jihar ce."

Sai dai ya kuma hango wasu matsaloli da yake tunanin zasu iya tasowa duba da girman ofishin da take riƙe da shi a matsayin uwar gidan gwamna.

"Sai dai kuma, ba'a nan gizo ke saƙar ba. Tana iya zuwa koyarwar duk sadda take da aji ko kuwa sai ta samu lokaci? Sanin kowa ne, Jami'a tana da tsare-tsare."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

"Kama daga lokacin shiga aji, abinda kowanne malami zai koyar da kuma suwaye zasu koyar. A ƙarƙashin wannan ina tababar cika wannan ƙa'ida daga wajen Matar Mai-girma gwamna duba da matsayinta da kuma ofishin da take riƙe dashi."

Gwamnan Delta Oborevwori Ya Nada Dan Takarar YPP a Babban Mukami

A wani rahoton kuma Gwamna Oborevwori na PDP ya naɗa ɗan takarar Jam'iyyar adawa a matsayin mai ba shi shawara ta musamman a jihar Delta.

Wannan na zuwa ne sama da wata ɗaya bayan gwamnan ya naɗa ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP a matsayi mai gwaɓi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262