Tinubu Na Duba Yiwuwar Nada ‘Dan Shekara 71 Ya Shugabanci Hukumar Yaki Da Rashawa

Tinubu Na Duba Yiwuwar Nada ‘Dan Shekara 71 Ya Shugabanci Hukumar Yaki Da Rashawa

  • Akwai yiwuwar Bola Ahmad Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar ICPC da zai canji Farfesa Bolaji Owasanoye
  • Abdu Aboki ne wanda shugaban kasa ya ke tunanin aika sunansa zuwa ga majalisar dattawa domin a tantance shi
  • Tsohon alkalin ya yi ritaya daga kotun koli a shekarar 2022, ya karanci ilmin shari’a a jami’ar ABU da ta Washington

Abuja - Bola Ahmad Tinubu ya na tunanin dauko tsohon Alkalin kotun koli, ya nada shi a matsayin sabon shugaban hukumar ICPC ta kasa.

A rahoton Premium Times aka samu labari cewa Mai girma shugaban kasa ya kyalla idanunsa kan Abdu Aboki kan batun shugaban ICPC.

Abdu Aboki wanda asalinsa mutumin Kano ne ya yi ritaya daga kotun koli a Agustan 2022 a sakamakon cika shekara 70 a kan bakin aiki.

Kara karanta wannan

"Mu Na Daf Da Durkushewa", NNPC Ya Tura Sako Ga Tinubu Kan Cire Tallafi Mai A Kasar

Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada Shugaban ICPC Hoto: Nosa Asemota
Asali: Twitter

Watakila tsohon alkalin ne zai maye gurbin Bolaji Owasanoye wanda zai bar ofis a 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin mutane da rikon ICPC

Rahoton ya ce ba wannan ne karon farko da tsoho ya jagoranci hukumar ICPC ba, shugabanta na farko, Mustapha Akanbi misali ne.

A lokacin da Olusegun Obasanjo ya nada Mustapha Akanbi bayan kafa ICPC, ya na da shekaru 68, ya yi ritaya daga kotun daukaka kara.

A 2005 Emmanuel Ayoola ya zama shugaban hukumar ya na shirin cika shekara 72, shi ma ya yi ritaya ne a kotun koli a Oktoban 2003.

Aboki zai iya zama Shugaban ICPC?

Abin da doka ta ce shi ne kafin mutum ya iya zama shugaban ICPC, dole sai ya cika sharadin zama alkali a babban kotun Najeriya.

Baya ga haka, sashe na 6 na dokar da ta kafa hukumar ta wajabtawa shugaban kasa aikawa majalisar dattawa sunan mutum mai daraja.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abin Da Ya Sa Tinubu Ya Yi Wuf Ya Nada Sababbin Mukamai 5

Aboki ya cika duk wasu sharuda tun daga aikin shari’a na sama da shekaru 10 zuwa rikon amana, sai dai wasu na ganin ya tsufa da yawa.

Karatu da aikin Mai shari'a Abdu Aboki

Dattijon da mai dakinsa ce Alkalin alkalai ta Kano ya yi karatu a jami’ar ABU Zariya da Washington, ya yi aiki a wurare da-dama a Najeriya.

Alkalin ya jagoranci shari’ar zaben gwamnan Legas a lokacin Bola Tinubu. Daga baya ya zama alkali a kotun daukaka kara da na kotun koli.

Wa zai canji Abdulrasheed Bawa a EFCC?

Fadar Shugaban kasa ta kammala shirin nada sabon Shugaba a Hukumar EFCC a Najeriya, Bola Tinubu zai maye gurbin Abdulrasheed Bawa.

Rahoton da aka samu ya nuna watakila a dawo da wani tsohon Sakatare wanda Muhammadu Buhari ya kore tare da Ibrahim Magu a 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng