Buhari ya rantsar da Farfesa Owasanoye sabon shugaban hukumar ICPC

Buhari ya rantsar da Farfesa Owasanoye sabon shugaban hukumar ICPC

A yau Litinin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da mambobi da kuma sabon shugaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, Independent Corrupt practices and other related Offences Commission.

Fadar shugaban kasa cikin wata sanarwa a yau Litinin 4 ga watan Fabrairu ta bayyana cewa, Farfesa Bolaji Owasanoye shine sabon shugaban hukumar ICPC wanda a baya ya kasance babban sakataren kwamitin bayar da shawara ga shugaban kasa akan harkokin rashawa.

Cikin zayyana jawaban sa na karbar ragamar jagoranci, Farfesa Owasanoye ya ce ba bu masakar tsinke ta rashawa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari da a yanzu mahandama da 'yan babakere sun gaza samun kofa ko wani sukuni na yasar dukiyar kasa da al'umma.

Farfesa Bolaji Owasanoye; sabon shugaban hukumar ICPC

Farfesa Bolaji Owasanoye; sabon shugaban hukumar ICPC
Source: UGC

Ya ke cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi tsayuwar daka wajen haramtawa masu tatsar dukiyar al'ummar kasar nan samun wani sukuni ko wata mafaka ta cin karen su ba bu babbaka kamar yadda ta kasance a gwamnatin baya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Farfesa Owasanoye ya yi wannan furuci yayin wani taron karawa juna sani da aka gudanar sanadiyar tsare-tsaren gwamnatin Buhari kan harkokin da suka shafi kasashen ketare daga 2015 kawo yanzu.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an gudanar da wannan babban taro a cibiyar kula da harkokin kasa-da-kasa ta Najeriya dake jihar Legas a ranar Alhamis 31 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki.

KARANTA KUMA: N200,000 na sayar da jariri na domin na kama sana'a - Wata Uwa ta gurfana gaban kotu

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kungiyar magoya bayan Buhari ta Forward with Buhari (FWB), ta ce ba bu wani mafificin a yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu face shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jagoran kungiyar na kasa, Sanata Lawal Shu'aibu, wanda ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa reshen Arewa, shine ya zayyana hakan a yau Litinin yayin ganawar sa da manema labarai cikin garin Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel