Yan Sanda Sun Ceto Mutane 171 da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Katsina

Yan Sanda Sun Ceto Mutane 171 da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Katsina

  • Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun sheƙe yan bindiga huɗu, sun ceto mutane sama da 170 da aka yi garkuwa da su
  • Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce jami'ai sun kuma kwato muggan makamai da dabbobi da babura da aka sace
  • Ya bayyana cewa 'yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban sama da mutum 1000

Jihar Katsina -Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun kashe mutum biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a tsakanin 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga Satumba, 2023.

Ta kuma bayyana cewa dakarun 'yan sanda sun ceto mutane 171 da aka yi garkuwa da su a lokuta daban-daban a tsawon wannan lokaci, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Yan sanda sun samu nasara mai yawa a wata 4 a Katsina.
Yan Sanda Sun Ceto Mutane 171 da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Katsina Hoto: PoliceNG
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen Katsina, ASP Abubakar Aliyu, shi ya bayyana haka ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

'Dalibai Mata Na Jami'ar Arewa da 'Yan Bindiga Suka Sace Sun Shaƙi Iskar 'Yanci, Bayanai Sun Fito

Kakakin 'yan sandan ya yi jawabi ne a madadin kwamishinan 'yan sandan jihar, Aliyu Musa a hedkwatarsu da ke Katsina yayin nuna wasu da ake zargi da aikata laifuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun ƙwato makamai da kayan sata

ASP Aliyu ya kara da cewa rundunar ta samu nasarar kwato bindigu kirar AK 47 guda hudu, bindigogi na gida guda shida, da kuma harsasai masu rai 517.

Bugu da ƙari, ya ce dakarun 'yan sandan ba su tsaya iya nan ba, sun kwato dabbobi 600, babura da motoci 12 da aka sace a tsawon wannan lokaci wata 4.

Ya kuma yi bayanin cewa, an kama mutane 1,005 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a ƙorafe-ƙorafe 853 da aka shigar a tsawon lokacin.

Kakakin 'yan sandan ya ce 395 daga cikin waɗan nan ƙorafe-ƙorafen yanzu haka suna gaban Kotu ana shari'a domin hukunta masu laifin, rahoton Punch ya tattaro.

Kara karanta wannan

Mu 100 Mu Ka Auka Makaranta, Aka Yi Awon Gaba da Yara a 2021 – ‘Dan Bindiga

“Mun kama mutane 707 da ake zargi da laifuka daban-daban kamar ta'addanci, cin zarafi, muggan kwayoyi, 'yan kungiyar asiri, tada hankali da gungun ‘yan bindiga, da sauransu."

Wani Malami a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja, ɗaya daga cikin inda lamarin rashin tsaro ya shafa ya faɗa wa wakilinmu cewa har yanzun akwai rina a kaba.

Da yake tattauna wa da wakilin Legit Hausa, Malam Yusuf, ya nuna cewa duk da an samu nasara amma haka ba zai hana nan gaba ka sake jin an kai sabon hari ba.

"Jami'an tsaron mu suna kokari, tsakani da Allah muna jinjina musu amma ni matsalar tsaron nam tana ɗaure mun kai. Ta ya yan ta'addan nan suke iya ɓuya?"

NDLEA Ta Kama Wata Mata da Tulin Haramtattun Kwayoyi a Filin Jirgin Kano

A wani rahoton kuma Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata mai suna Bilkisu ɗauke da ƙunshin holar iblis sama da 50 a filin jirgin Aminu Kano.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wasu Garuruwa, Sun Halaka Babban Basarake a Jihar Arewa

A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA , Femi Babafemi, ya fitar, ya ce jami'ai sun cafke matar da ake zargin ne tun ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262