NDLEA Ta Kama Wata Mata da Tulin Haramtattun Kwayoyi a Filin Jirgin Kano
- Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata mai suna Bilkisu ɗauke da ƙunshin holar iblis sama da 50 a filin jirgin Aminu Kano
- A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an kama matar ne yayin da take shirin kama jirgi zuwa ƙasa mai tsarki ranar Talata
- NDLEA ta ƙara da bayyana yadda ta kama wasu da haramtattun kwayoyi a jihar Oyo da titin Bauchi zuwa Gombe
Jihar Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta damƙe wata mata ɗauƙe da ƙunshin hodar iblis 52 a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NDLEA ta kama matar mai suna, Bilkisu Mohammed Bello, yayin da take yunkurin kama jirgi zuwa ƙasar Saudiyya.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, ya ce jami'ai sun cafke matar da ake zargin ne tun ranar Talata.
Sanarwan ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A yayin da ake zantawa da ita, ta amsa cewa kwalayen hodar iblis da aka ba ta ta hadiye kafin lokacin tashin jirgin nata an ajiye su ne a wani gida da ke unguwar Farawa a Kano."
"Lokacin da ta jagoranci jami'an hukumar NDLEA zuwa gidan, an samu ƙunshi 52 na haramtattun kayan da nauyinsu ya kai giram 767."
Wasu nasarorin da NDLEA ta samu a Najeriya
Haka nan kuma sanarwan ta ƙara da bayyana wasu nasarorin da jami'an hukumar NDLEA suka samu a wasu sassan jihohin Najeriya.
A rahoton jaridar PM News, sanarwan NDLEA ta ƙara da cewa:
“Haka nan kuma, an kama wani da ake zargi mai suna, Auwal Bindow, a kan titin Bauchi zuwa Gombe ranar Juma’a ɗauke da maganin turamol 50,000."
"A jihar Oyo, jami’an NDLEA da ke sintiri a titin Legas zuwa Ibadan, sun kama Anuoluwapo Blessing Iyanu, mai shekaru 32, da kwalaye 52 na wiwi sativa mai nauyin kilogiram 30 a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba."
Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa
A wani rahoton na daban kuma Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Kogi yayin da zaɓen gwamna ke ƙara kusantowa a wata mai zuwa.
Yahaya Ododo, ya yi murabus daga mamban jam'iyyar APC, kana ya koma AA domin mara wa ɗan takarar jam'iyyar baya.
Asali: Legit.ng