Gwamnatin Bauchi Za Ta Biya Dalibai Mata Kudi Su Rika Zuwa Makaranta
- Gwamnatin jihar Bauchi ta shirya fara biyan ɗalibai mata kuɗaɗe masu tsoka a kowane zangon karatu
- Gwamnatin za ta riƙa biyan kuɗaɗen ne domin ganin yara mata waɗanda iyayensu ba su da ƙarfi sun riƙa zuwa makaranta
- A ƙarƙashin shirin na biyan kuɗaɗen, ɗalibai mata na ƙananan sakandire za su samu N5000, na manyan sakandire kuma N10,000
Jihar Bauchi - A wani ɓangare na ƙoƙarin inganta halartar yara mata zuwa makaranta, jihar Bauchi za ta biya ɗalibai mata 16,260, naira 5,000 da 10,000 a kowane zangon karatu a faɗin makarantun jihar.
Biyan kuɗin na daga cikin wani ɓangare na shirin 'Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment' (AGILE), cewar rahoton Premium Times.
Na wa za a rika biyan ɗaliban?
Kwamishiniyar Ilimi, wacce ita ce ke kula da shirin na AGILE, Jamila Dahiru, ta shaida wa manema labarai a ranar Asabar cewa, gwamnati za ta biya ƴan mata a ƙananan makarantun sakandire, naira 5000 a kowane zangon karatu, sannan wadanda ke manyan makarantun sakandare za a rika biyan su naira 10,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jamila Dahiru ta ce shirin na AGILE yana da nufin yin abubuwa daban-daban domin inganta ilimi a jihar, rahoton Blueprint ya tabbatar.
A kalamanta:
"Shirin dai na da nufin taimakawa ɗaliban da suka daina zuwa makaranta saboda matsalolin rashin abun hannu."
"Waɗannan ɗaliban suna da damar komawa makaranta kuma su kammala mataki na biyu na ilimi."
"Waɗanda ake son samu su ne talakawa tukuf waɗanda ba su da hanyar biyan kuɗin makaranta da sauran abubuwan da ake buƙata, an sanya matakan da za a bi domin gano waɗanda suka cancanta."
"Bayan ƙara yawan ɗalibai mata a makarantu, shirin AGILE zai tabbatar cewa ingantaccen ilmin da ake bayarwa bai ragu ba, a maimaikon hakan sai dai ya ƙaru domin za a ƙara ƙarfafa gwiwar malamai da samar musu da kayan aikin da za su koyar da ɗalibai."
Gwamnatin Neja Za ta Farfado Da Biyan Tallafin Karatu
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Neja a ƙarƙashin gwamna Umaru Bago, ta ce zata farfaɗo da tsarin biyan ɗalibai tallafin karatu.
Gwamnatin za ta dawo da tsarin ne na tallafawa ɗaliban da ke karatu a jami'o'i da kuɗaɗe domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng