Gwamnatin jahar Kaduna ta ware naira biliyan 1.8 don biyan tallafin karatu

Gwamnatin jahar Kaduna ta ware naira biliyan 1.8 don biyan tallafin karatu

Shugaban hukumar bada tallafin karatu na jahar Kaduna, Jummai Dikko ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kaduna ta ware naira biliyan 1.8 don biyan dalibai kudin tallafi tare da daukan nauyin wasu daliban jahar don karatu a kasashen waje.

Dikko ta bayyana haka ne yayin da take ganawa da manema labaru yayin wani taro na Islamic Education Initiative a garin Zaria na jahar Kaduna, inda tace daga cikin kudin gwamnati ta ware naira biliyan 1 don daukan nauyin masu fita kasa waje.

KU KARANTA: Masha Allah: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya cika shekaru 63 a rayuwa

“A yanzu haka gwamnatin Kaduna ta ware naira miliyan 800 don baiwa daliban dake karatu a Najeriya tallafi, duk a cikin kasafin kudin shekarar 2019. Daga cikin kudin mun kashe naira miliyan 774, inda muka baiwa N100,000.

“Wannan ya saba ma yadda ake biyan tallafin karatu N15,000 a baya a jahar Kaduna, amma tun bayan zuwa gwamnan jahar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya kara adadin kudin zuwa N100,000.” Inji ta.

Hajiya Dikko ta cigaba da cewa gwamnatin jahar Kaduna ta dauki nauyin dalibai masu karatun likitanci a kasar Cuba inda zasu kwashe shekaru 6, inda tace suna fatan daliban zasu kammala karatun har zu zama likitanci.

“A yanzu haka mun ware naira miliyan 300 don biyan kudaden karatunsu har su gama, mun yi haka ne don gudun samun tsaiko a karatunsu a sakamakon canjin gwamnati ko canjin shugabanci.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel