Mai Fafutukar Kafa Kasar Yarbawa, Igboho Ya Shaki Iskar ’Yanci a Jamhuriyar Benin

Mai Fafutukar Kafa Kasar Yarbawa, Igboho Ya Shaki Iskar ’Yanci a Jamhuriyar Benin

  • Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa ya samu ‘yanci bayan shafe shekaru biyu ya na tsare
  • An kama Igboho ne a watan Yuli na shekarar 2021 yayin da ya ke shirin tserewa zuwa kasar Jamus
  • Igboho bayan fitowarshi a Jamhuriyar Benin, ya godewa Olusegun Obasanjo da Farfesa Akintoye kan goyon bayansu

Cotonou, Benin - Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho Adeyemo ya shaki iskar ‘yanci daga Jamhuriyar Benin.

Legit ta tattaro cewa shugaban Gamayyar Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye shi ya bayyana haka a jiya Lahadi 8 ga watan Oktoba.

Igboho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa ya samu 'yanci a Benin
Igboho Ya Shaki Iskar ’Yanci a Jamhuriyar Benin. Hoto: Facebook.
Asali: UGC

Yaushe Igboho ya samu 'yanci?

Akintoye ya ce Igboho ya samu ‘yancin ne a jiya Lahadi a Jamhuriyar Benin inda ya ce zai wuce kasar Jamus don haduwa da iyalansa bayan shafe shekaru biyu a tsare.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Tsige Firayim Minista, Ya Rusa Majalisarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PM News ta tattaro cewa an kama Igboho ne a watan Yuli na shekarar 2021 yayin da ya ke shirin hawa jirgin sama don zuwa kasar Jamus mako daya bayan ya sha da kyar daga hannun jami’an tsaro a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo.

Bayan faruwar lamarin, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ayyana Igboho a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo yayin da ya yi kokarin zillewa zuwa kasar Jamus.

Bayan an sake shi daga magarkama, Igboho ya tabbatar da samun ‘yancin nasa inda ya ce ya cika dukkan sharudan ba da beli kuma zai dawo Najeriya nan kusa.

Meye Igboho ya ce bayan fitowarshi?

Ya ce:

"Ina tabbatar muku da cewa yanzu na samu ‘yanci kuma zan dawo Najeriya, kuma na cika dukkan sharuda.
“Duk da cewa ina rayuwa a Cotonou na wani lokaci, yanzu haka na samu ‘yancin barin Cotonou zuwa Najeriya.”

Kara karanta wannan

Shugabannin Jam'iyya 21 da Jiga-Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa, Sun Faɗi Abinda Ya Ja Hankalinsu

A cikin wani faofan bidiyo da aka yada a kafar sadarwa, Igboho ya godewa jama’a musamman wadanda su ka ba shi gudumawa ta ko wane bangare yayin zamansa a Benin.

Faifan bidiyon da Tribune ta yada, an gano Igboho na godiya ga Farfesa Banji Akintoye da kuma Cif Olusegun Obasanjo da goyon bayansu.

Koru ta yi hukunci kan Sunday Igboho da matarsa

A wani labarin, Kotun da ke zamanta a Jamhuriyar Benin ta yi hukunci inda ta umarci sake matar dan awaren Yarbawa, Sunda Igboho.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kotun ta umarci mayar da Igboho gidan yari don ci gaba da zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.