Tinubu Zai Dawo Da Shirin ‘Tradermoni’ Don Tallafawa Kananan ’Yan Kasuwa Da Kawar Da Talauci
- Shugaba Tinubu ya dawo da shirin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari don rage radadin talauci a kasa
- Tinubu ya dawo da shirin ne na ‘Tradermoni’ wanda ake bai wa kananan ‘yan kasuwa rance don tallafawa kasuwancinsu
- Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ta ce a wannan karo Naira dubu 50 masu cin gajiyar za su samu na lamuni
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta dawo da shirin ‘Tradermoni’ na tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Nuwamba.
Wannan karo masu cin gajiyar shirin za su samu Naira dubu 50 don taimakawa harkokin kasuwancinsu madadin dubu 10 da a baya ake ba su.
Meye Tinubu ya ce kan shirin 'Tradermoni'?
Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ita ta bayyana haka a gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi 8 ga watan Oktoba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta tattaro cewa an kaddamar da shirin ‘Tradermoni’ ne a shekarar 2018 don rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Yayin sanar da dawo da shirin, Edu ta ce:
“A yanzu karon farko, a watan Nuwamba za mu zabi babbar kasuwa a mazabu uku da mu ke da su a ko wace jihar don ba da tallafin ga ‘yan kasuwa.”
Wane tsari Tinubu ya dauko na shirin?
Edu ta ce wadanda za su ci gajiyar shirin za a zabe su ne ba tare da bambanci na jam’iyya ko kuma wani alfarma ba a cikin al’umma.
Ta ce bayan an zabi masu cin gajiyar, za a bude musu asusun banki wanda za su samu kudadensu ta ciki daga Babban Bankin Najeriya, CBN.
Har ila yau, Edu ta ce wadannan kudade da za a bayar babu kudin ruwa a ciki kuma duk wadanda su ka biya za su samu damar karin wasu kudaden a gaba.
Ta tabbatar da cewa wannan shiri ba shi da alaka da siyasa kuma an kirkiri shirin ne don tallafawa mutane kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu a kan haka.
Tinubu ya dakatar da shirin N-Power
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya dakatar da shirin N-Power har sai baba-ta gani saboda wasu matsaloli.
Ministar jin kai da walwala Dakta Betta Edu ta bayyana cewa akwai tarun matsaloli wanda sai an yi kwakkwaran bincike a kansu.
Asali: Legit.ng