An Kashe Mutum 4, An Kwamushe 5 a Harin ’Yan Bindiga a Zaria, Rahoton 'Yan Sanda

An Kashe Mutum 4, An Kwamushe 5 a Harin ’Yan Bindiga a Zaria, Rahoton 'Yan Sanda

  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana yadda tsagerun 'yan bindiga suka kai farmaki tare da hallaka wasu mutane
  • An kama tsagerun da ake zargin sun aikata laifin satar mutane, ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin
  • Jihohin Arewa maso Yamma na ci gaba da fuskantar zubar jini yayin da tsagerun 'yan bindiga ke kara kamari

Zaria, Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane hudu a wani harin da aka kai a daren Juma’a a Ungwan Dankali da ke karamar hukumar Zaria.

Jaridar The Nation ta ruwaito daga majiyoyin cikin gida cewa an kashe mutane biyar a yayin harin.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta ce jami’anta tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su tare da kama wani da ake zargin dan bindiga ne.

Kara karanta wannan

Abokai 5 Sun Mutu Tare a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

An kama 'yan ta'ada bayan sata a Zaria
Yadda aka kama tsageru a Zaria bayan kai hari | Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Yadda 'yan sanda suka kai dauki

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Musa Yusuf Garba, ya ce a lokacin da suka karbi kiran gaggawakan farmakin, jami’an ‘yan sandan shiyyar Dan magaji sun kai dauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya ce sun samu taimakon sashen 'yan sandan yankin Zaria, wanda nan take suka dunguma wurin da lamarin ya faru, Channels Tv ta ruwaito.

A cewarsa, sun samu mutum shida aka jikkata a yayin harin, wanda tuni aka kai su asibitin don jinyar gaggawa.

Wadanda aka jikkata sun mutu

Ya kuma bayyana cewa, bayan wadanda jikkatan zuwa asibitin Muslim, likitoci sun alanta mutuwar hudu daga cikinsu nan take.

'Yan sanda sun kuma ce a halin yanzu wadanda aka kaman suna ci gaba da ba jami'ai hadin kai don yin bincike cikin tsanaki da kai wa ga abokan harkallarsu.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Yi Kazamin Artabu da 'Yan Fashi, An Harbi Insufekta da Wasu Masu Gadi

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke yawan fama da farmakin 'yan ta'adda, musamman tun shekarar 2021.

An sace ma'aikatan titi a Kaduna

An shiga jimami yayin da aka sake awon gaba da wasu mutane a ma'aikatan kamfanin da ke titin hanyar Kaduna zuwa Kano.

An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Tashar Yari da ke karamar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna.

Tun 2021 'yan bindiga ke ci gaba da addabar mutane a yankunan Kaduna da ma sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.