Zaria: 'Yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidajen lakcarorin ABU, sun yi awon gaba da Farfesa
- Rahotannin kwanakin baya bayan na na nuni da cewa 'yan bindiga sun fara matsawa garin Zaria
- Wasu 'yan bindiga sun kai hari kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bammali a garin Zari a makon da ya gabata
- A karshen makon da ya gabata, rahotanni sun sake kawo labarin yadda aka sace daliban jami'ar ABU har guda 9
Wasu 'yan bindiga dadi sun kutsa kai zuwa cikin rukunin gidajen malaman jami'ar ABU da ke Zaria, jihar Kaduna, tare da yin awon gaba da Dakta Bako, Farfesa a bangaren ilimin sani aikin jikin dan adam (Physiology)
Auwalu Umar, darektan hulda da jama'a na jami'ar ABU, ya tabbatar da kai harin, inda ya bayyana cewa 'yan bindigar sun dira gidan Farfesan da misalin karfe 12:50 na safiyar ranar Litinin.
A cewar jawabin da Umar ya fitar, 'yan bindigar sun yi awon gaba da Dakta Bako tare da matarsa da diyarsa, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
"Ofishin jami'an tsaro na Jami'a ya gaggauta sanar da jami'an rundunar 'yan sanda ma su bincike na musamman (IRT) kuma sun amsa kira tare da hanzarta zuwa wurin.
KARANTA: Tinubu ne ya aikasu su roki Buhari; Bode George ya fadi dalilin ziyarar dattijan APC zuwa Villa
"An yi musayar wuta a tsakanin jami'an 'yan sanda da 'yan bindigar. Bayan sun fahimci cewar an fi karfinsu, sai suka hanzarta fadawa cikin jeji tare da mutanen da suka sace.
"Jami'an 'yan sanda sun bi sahun 'yan bindigar har zuwa kauyen Sasuwar Da'a da ke makwabtaka da Jami'a.
"Ganin cewa 'yan sanda sun matsa musu lamba, sai 'yan ta'addar suka saki matar Farfesa Bako da diyarsa, shi kuma suka yi awon gaba da shi.
"An tsinci kwanson alburusai a wurin da aka yi musayar wuta da 'yan ta'addar," a cewar jawabin Umar.
KARANTA: Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari
Wanan sabon harin na zuwa mako daya kacal bayan wasu 'yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidajen malaman kwalejin kimiyya ta Nuhu Bamalli da ke garin Zaria.
Bayan harin da aka makarantar Nuhu Bamalli, wasu 'yan bindiga sun sake sace daliban jami'ar ABU guda 9 a karshen mako.
Kafin wallafa wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta wallafa labarin yadda wasu 'yan bindiga suka kutsa kai cikin gidan dan majalisar wakilai, Abubakar Kusada, a jihar Katsina.
Bayan shigarsu gidan, 'yan bindigar sun nemi ina mahaifiyar dan majalisar ta ke, kasancewar ba ta gidan, 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'yan uwan Honarabul Kusada guda biyu tare da raunata wani guda.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng