Sojoji Sun Sheke ’Yan Ta’adda 31, Sun Kama 81 a Cikin Mako Guda, Inji Hedkwatar Tsaron Najeriya

Sojoji Sun Sheke ’Yan Ta’adda 31, Sun Kama 81 a Cikin Mako Guda, Inji Hedkwatar Tsaron Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kadan daga ayyukan da suka yi a cikin mako guda a yankunan Arewacin Najeriya
  • An kama 'yan ta'adda tare da hallaka wasu da dama a daidai lokacin da suke ci gaba da barna a Arewa
  • 'Yan IPOB sun shigo yankin Arewa, sun gamu da fushin soji yayin da aka yi ram da su a jihar Benue

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce a cikin makon da ya gabata dakarun soji sun sheke ‘yan ta’adda 31 tare da kame 81 a hare-hare daban-daban a yankin Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa ta Yamma.

Daraktan yada labarain tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shekaru 20: Kotu Ta Yanke Wa Wadanda Suka Yi Garkuwa da Babban Lauya Hukunci Mai Tsauri

Buba ya ce sojojin sun kuma kubutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su yayin da ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP 63 da iyalansu suka mika wuya ga sojojin a aikin.

An ragargaji 'yan bindiga a Arewa tare da kama da yawa
An hallaka tare da kama 'yan ta'adda a Arewa | Hoto: Nigerian Defence Headquarters
Asali: Facebook

Aikin soji a Arewa maso Gabas

A yankin Arewa maso Gabas, ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun gudanar da aikin fatattakar 'yan ta'adda a kananan hukumomin Bama da Chibok a jihar Borno, da kuma karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana yadda sojojin suka kwace bindigogi kirar AK47 guda 12, bindigu hadin gida guda biyu da wasu nau'ikan guda uku, alburusai 181 na musamman masu girman 7.62mm, mujallu hudu, da babura uku da dai sauransu.

Ya kara da cewa sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 13, sun kama 12 tare da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Za a Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21 a Kan Mutuwar Mohbad

Arewa ta Taskiya da aikin da soji suka yi

A yankin Arewa ta tsakiya kuwa, ya ce dakarun Operation Safe Haven sun cafke mutane biyar tare da kwato makamai da alburusai, Leadership ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, ana zargin wadanda aka kaman ne da laifin sace shanu, wanda tuni aka kwato guda 145 duk dai a cikin makon.

An kama tsagerun IPOB

A bangare guda, ya ce dakarun Operation Whirl Stroke a ranar 1 ga Oktoba, sun kama wasu ’yan kungiyar ta'addanci ta IPOB/ESN guda biyu a karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue yayin da suke shirin aikata barna.

Ya bayyana cewa an kama 'yan ta'addan ne a gidan wani babban mai hada magungunan gargajiya, amma an ruwaito shi ya fece.

Daga nan, ya bayyana adadin kayayyakin aikata barna da aka kwace daga hannun wadannan masu aikata laifuka daban-daban a Najeriya.

Yadda aka ragargaji 'yan ta'adda a Arewa ta Yamma

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Maida Ma'aikata Sama da 700 da Gwamnati Ta Kora Daga Aiki, Zai Biyasu Albashi Tun 2018

A Arewa maso Yamma kuwa, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda shida, sun kama 12 tare da ceto mutane 33 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce sojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu, Danish guda biyu, harsasai 35 na musamman masu girman 7.62mm, babura uku, wayoyin hannu guda biyar, da sauran kayayyakin aikata laifi.

An kama kasurgumin dan ta'adda

A wani labarin, jami’an ‘yan sanda sun kama shugaban wata tawagar masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa a Damagum da ke Kolere da wasu sassan Tarmuwa da Dapchi a jihar Yobe.

An kama Mohammed Wada mai shekaru 35 dan kauyen Kanda ne a karamar hukumar Fune a unguwar Kolere da ke garin Fune, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan labari dai na fitowa ne daga rundunar 'yan sandan jihar, inda suka bayyana yadda aka kama tsagean.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel