Fetur @ N620: A Hakan, Gwamnati Ta Na Biyan Tallafin Man Fetur Inji PENGASSAN
- Kungiyar PENGASSAN ta fayyace halin da ake ciki wajen harkar fetur bayan ikirarin cire tallafi
- Festus Osifo ya ce a farashin da ake saida lita a gidan mai, shakka babu gwamnati ta na tallafawa
- Shugaban kungiyar masu harkar mai da gas na kasar ya tabbatar da abin da ake zargin ana yi a boye
Abuja - Shugaban kungiyar PENGASSAN ta masu harkar mai da fas, Festus Osifo ya ce gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin fetur.
An rahoto Kwamred Festus Osifo a tashar Channels ya na cewa har yanzu gwamnatin Bola Tinubu ba ta yi ban-kwana da tallafin fetur ba.
Dalilan kuwa su ne Dalar Amurka ta tashi a kan Naira, sannan farashin danyen mai ya karu yanzu.
Da aka yi hira da shi a tashar talabijin a ranar Juma’a, ‘dan kasuwan ya nuna farashin da ake sayen mai bai kai ainihin darajarsa a kasuwa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Man fetur: Matsayar kungiyar PENGASSAN
"Su (Gwamnati) su na biyan tallafin man fetur a yau
A hakikanin lamari a yau, akwai tallafi saboda a lokacin da aka yanke farashin nan, kudin gangar mai a kasuwar duniya ya na kusan $80 ne.
Amma yanzu gangan danyen man ta kai $93/94. Saboda haka, farashi ya canza, to ya kamata kudin litar man fetur (a gidajen mai) ya tashi."
- Festus Osifo
Matakan cire tallafin man fetur
Kafin gwamnati ta iya cire tsarin tallafin fetur gaba daya, Vanguard ta rahoto Festus Osifo ya na cewa sai an dauki wasu matakan tattalin arziki.
Shugaban na PENGASSAN ya ce abin da ya hana farashi canzawa shi ne idan aka kula da darajar kudi da kyau kuma za a samar da kudin waje.
Bayanin Osifo ya gaskata zargin da ake yi na cewa an dawo da tallafin fetur ta bayan fage.
Tsarin zai taimaka wajen rike farashin fetur tsakanin N615-N620 musamman a lokacin da mafi yawan mutane ke kukan mai ya yi tsada sosai.
Masani ya soki cire tallafin fetur
Usman Adamu Bello ya yi mana bayanin tasirin tsarin tattalin arzikin arzikin da aka kawo, ya ce cire tallafi da karya Naira su na da matukar hadari.
Masanin yana da digirin BSc, MSc da PhD a ilmin tattalin arziki kuma ya yi nazari da rubuce-rubuce kan abubuwan da su ka shafi tattali da darajar kudi.
Asali: Legit.ng