Jami’an ’Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Mutuwar Mawaki Mohbad a Jihar Legas
- A karshe an fadi dalilin mutuwar mawaki Ilerioluwa Oladimeji wanda aka fi sani da Mohbad a jihar Legas
- Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya bayyana sunan Ibrahim Owudunni da aka fi sani da Primeboy a matsayin wanda ake zargi
- Kwamishinan ya ce Mohbad da Primeboy sun yi mummunan fada inda Mohbad din ya samu raunuka a kansa
Jihar Legas – Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, Idowu Owohunwa ya bayyana dalilin mutuwar mawaki Ilerioluwa Oladimeji da aka fi sani da Mohbad.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a yau Juma’a 6 ga watan Oktoba yayin ganawa da manema labarai a Ikeja da ke jihar, Legit ta tattaro.
Meye dalilin mutuwar mawaki Mohbad?
Ya ce dalilin mutuwar mawakin ya samu ne sanadiyyar fada da su ka yi da amininsa na kut-da-kut mai suna Ibrahim Owudunni da aka fi sani da Primeboy, cewar The Guardian.
Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Yi Karin Bayani Kan Mutuwar Mawakin Najeriya, Sun Bayyana Mutum 5 Da Ake Zargi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa Mohbad da Primeboy sun yi fadan ne a Ikorodu yayin wani bikin mawaka inda Mohbad ya samu raunuka a kansa wanda ya yi sanadinshi.
A cewarsa:
“A karshen bikin mawakan, Mohbad da Primeboy sun yi mummunan fada inda Mohbad ya samu raunuka a kansa.
“Da ya ke ba a kula da raunukan yadda ya kamata ba, hakan ya yi sanadin mutuwarshi, don haka Primeboy ya zama wanda ake zargi da kisa.
Cikakken bayani daga jami'an 'yan sanda
Kwamishin ya yi cikakken bayanin yadda Mohbad ya mutu cikin faifan bidiyon da jaridar Punch ta yada.
Mutuwar Mohbad ta jawo cece-kuce inda 'yan Najeriya su ka yi ta zanga-zanga a fadin kasar don a binciko dalilin mutuwarshi.
Ku kalli bidiyon a kasa:
Jami'an tsaro da na lafiya sun tono gawar Mohbad
A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a jihar Legas tare da hadin gwiwar jami'an lafiya sun tono gawar mawaki, Ilerioluwa Aloba, da aka fi sani da Mohbad.
Kakakin rundunar a jihar, SP Benjamin Hundeyin, shi bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar 21 ga watan Satumba a Ikeja da ke Legas.
Hundeyin ya ce an tono gawar mawakin ne don fara bincike kan mutuwar tasa da ake ta zargin ba haka kawai ya mutu ba.
Asali: Legit.ng