Tattalin Arziki: Naira Ta Shiga Cikin Sahun Kudi Mafi Rashin Daraja a Duk Afrika
- A kasashen da ke Afrika, babu kudin da su ka rasa darajarsu a shekarar nan irin Naira da Kwanza
- Rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya yi bayani mai tsoratarwa game da tattalin arzikin Najeriya
- Baya ga Najeriya mai arzikin mai, kudin kasashen Congo, Zambiya, Ghana da Ruwanda sun karye
Abuja - Babban bankin Duniya ya kawo kudin Najeriya na Naira a cikin kudin da darajarsu su ka fi kowane karyewa a Afrika.
The Cable ta ce darajar Naira da kudin Angola watau Kwanza ya na karyewa sosai, sun zama abin Allah-wadai a nahiyar Afrika.
A shekarar 2023, Naira da Kwanza sun rasa kusan 40% na darajarsu a sakamakon dalilai da-dama.
Babban bankin ya ce matakin da bankin Najeriya na CBN ya dauka na cire takunkumi wajen kasuwanci ya nakasa Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Larabar nan ne bankin duniyan ya fitar da rahoton kasashen Afrika kamar yadda ya saba yi sau biyu a kowace shekara.
Sauran kudin da su ka karye
Karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya da yawan bashi da ake bin Angola ya taimaka wajen karya Kwanga.
Sauran kudin da su ka karye a shekarar nan sun hada da fam na kasar Kudancin Sudan, Burundi Franc (BIF) da Kenyan Shilling.
Sauran kudin da su ka rasa darajarsu sun kunshi: Congolese Franc, Kwaca ta Zambiya, Cedi ta Ghana da kudin Ruwanda.
Sai Najeriya ta rage buga Naira
A rahoton, bankin duniya ya ja-kunnen Najeriya da Ethiopia da su rage yawan buga kudi, abin da masana sun koka a kai a baya.
Wani kuskure da masana su ke zargin kasashen Afrika su na yi sun hada da rashin tsari wajen fito da tsare-tsare da sunan bada tallafi.
Bankin ya yi kira ga gwamnatocin nahiyar su yi hattara da tsare-tsaren kudin kasashen waje domin tsare darajar kudin gida.
Har ila yau, an gargadi irinsu Najeriya da Ghana a kan tsadar kaya, wanda hakan ya na da mummunan tasiri a kan tattalin arziki.
Fetur zai iya tashi a Najeriya
An samu karin akalla N70 a kan kudin da ‘yan kasuwa su ke sayen fetur a tashoshi, hakan zai iya jawo kudin litan mai ya sake tashi.
An rahoto Shugaban NOGASA ya na cewa tasoshi da yawa sun bushe kar-kaf, hakan ya nuna fetur ya fara yankewa yanzu a Najeriya.
Asali: Legit.ng