Yan Sanda Sun Yi Karin Bayani Kan Mutuwar Mawaki Mohbad, Sun Bayyana Mutum 5 Da Ake Zargi

Yan Sanda Sun Yi Karin Bayani Kan Mutuwar Mawaki Mohbad, Sun Bayyana Mutum 5 Da Ake Zargi

  • Har yanzu rundunar yan sandan Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike a kan mutuwar makwai Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad
  • Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Idowu Owohunwa, ya yi jawabi a ranar Juma'a inda ya yi karin haske kan inda suka kwana a bincike kan mutuwar mawakin
  • Owohunwa ya ce zuwa yanzu sun samu shaidu 26 sannan sun yi wa mutane biyar da ake zargi da hannu a mutuwar tambayoyi

Jihar Lagas - Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Idowu Owohunwa, ya yi karin haske game da binciken da ke gudana kan marigayi mawakin Najeriya, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

A wani taron manema labarai da Legit Hausa ta bibiya a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, hukumar yan sandan ta bayyana cewa zuwa yanzu an gano wasu shaidu 26, kuma suna taimakawa da bayanai kan mutuar mawakin.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Hadu Da Saurayin Da Ya Yi Tattaki Daga Amurka Don Ganinta a Karon Farko a Bidiyo

Yan sanda sun yi karin haske kan mutuwar mawaki Mohbad
Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Mutuwar Mawaki Mohbad, Sun Bayyana Mutum 5 Da Ake Zargi Hoto: Mohbad
Asali: Instagram

Kwamishinan yan sandan ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu an yi wa akalla mutum biyar da ake zargi tambayoyi.

Owohunwa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zuwa yanu an gano shaidu 26 a binciken da ke gudana na Mohbad.

"Zuwa yanzu an yi wa mutum biyar da ake zargi tambayoyi a binciken da ke gudana."

Mohbad: ‘Yan sanda za su tsare mawaka, Naira Marley da Sam Larry na kwana 21

A baya mun ji cewa wata kotun majistare da ke zama a Yaba a jihar Legas ta amince a tsare Azeez Fashola da Balogun Eletu a hannun ‘yan sanda.

Tribune ta ce alkaliyar da ta yi hukunci a ranar Laraba ta ba jami’an tsaro damar rike Naira Marley da Sam Larry domin a iya binciken su.

Domin a kammala duk binciken da ake yi a game da mutuwar mawakin nan, Ilerioluwa Aloba, ‘yan sanda su na bukatar kwanaki 30.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashin Tashoshi Ya Zarce N720

Mohbad: Primeboy ya mika kansa ga yan sanda bayan ayyana nemansa ruwa a jallo

Duk a kan mutuwar mawakin, mun kuma ji cewa Owodunni Ibrahim wanda aka fi sani da Primeboy wanda ake nema ruwa a jallo kan mutuwar Oladimeji Aloba watau Mohbad ya mika kansa ga ‘yan sanda.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta ayyana nemansa ruwa a jallo kuma ta sanya ladan Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng