“Ladidin Baba”: Uba Ya Fashe Da Kuka Ba Kakkautawa a Wajen Bikin Diyarsa, Bidiyon Ya Yadu
- Wani bidiyo mai tsuma zuciya ya nuno wani uba yana sharban kukan farin ciki a ranar auren diyarsa ya yadu a soshiyal midiya
- Mutumin ya kasance zaune kusa da diyarsa, wacce ta kasance amaryar, yayin da matarsa, wacce ita ce uwar amaryar ke murmushin farin ciki a daya bangaren
- Mahaifin amaryar ya gaza boye karayar da zuciyarsa ta yi yayin da ya dungi kuka ba kakkautawa, inda diyar tasa ta taya shi
Wani bidiyo mai tsuma zuciya da ke nuna wani uba dan Najeriya cikin hawaye a ranar auren diyarsa ya tsuma zukatan masu kallo da dama a soshiyal midiya.
Mahaifin ya kasance zaune kusa da diyar tasa, wacce ke sanye da rigar amare, yayin da matarsa wacce ta kasance uwar amaryar ke ta murmushin farin ciki a daya bangaren.
Zuciyar mahaifin amaryar ya karaya yayin da ya dungi zubar da hawaye, yana mai nuna tsantsar soyayyarsa da alfahari da diyar tasa.
Lamarin ya taba zuciyar diyar tasa inda ita ma ta fashe da kuka. Hadadden bidiyon ya nuna shakuwar da ke tsakanin uba da diyarsa da kuma farin cikin uwa wacce ta ga dakin diyarta lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani ga bidiyon mahaifin da ke kuka a ranar bikin diyarsa
Bu_Bu ta ce:
"Mahaifina zai yi kuka ya ji babu dadi a ranar aurena. Allah ya albarkaci gidan aurenki."
Adetutu ta rubuta:
"Na tayaki murna, ina ma ace mahaifina yana raye har yanzu ina kewarka mahaifina."
Teelah ta yi martani:
"Idan diyar kirki tana aure."
Apekev ta yi martani:
"Diyar babanta na tayaki murna."
Patricia Creations:
"Baba na kuka saboda ba zai iya kai mata ziyara ya kwana ba amma mama za ta iya. Allah ya albarkaci daukacin ubanni masu kula da yaransu."
Wata Uwa Ta Fashe Da Dariya Ba Kakkautawa Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karo Na Farko, Faifan Muryar Ya Yadu
Aje wamiri:
"Zan yi aure kwanan nan amma babu mahaifi."
Matar aure ta yi rawar murna bayan surukarta ta ziyarce ta
A wani labari na daban, wata matar aure da ke matukar kaunar uwar mijinta ta taka rawa jim kadan bayan isowarta gidansu don yin kwana biyu da su.
Matar wacce ta cika da farin ciki ta gaza boye murnarta yayin da ta taka rawa iri-iri, tana girgijewa don nuna yadda ta ji dadin ganinta.
Asali: Legit.ng